20/11/2025
Lokaci yayi daya kamata mu bayyana matsayarmu a siyasar kawaji ward da karamar hukumar Nassarawa.
Lokaci yayi daya kamata Al'ummar mazaɓar kawaji dama karamar hukumar Nassarawa su tashi tsaye wajen neman mafita ta siyasa kafin lokacin zaɓe ya ƙaraso yan tayi daɗi da mayaudaran Al'umma su baza komarsu don ribatar Al'ummar mu. A zaɓe su tafi Abuja ko majalissar jaha batare da amfanawa kowa komai ba, wanda dagasu sai ƴan korensu suke amfana.
A wannan gaɓa, dole mutashi mu yaƙi yan cika tsere na siyasa muɗauko jajirtattun da zasu taimaki Al'ummar mu, musamman samarwa matasa aikinyi a Gwamnati, kamfanoni,koyar da Sana'o'i da raba jari mai ƙarfi bana bogi ba.
Mun kammala nazari ga ƴan siyasar mu tun daga kan House of Rep, State Assembly dama ɗaiɗaikun mutane a siyasa da irin gudummawar da s**a bawa Al'ummar mu. Za'aji matsayarmu insha Allah lokaci kaɗan.
Bissalam 🙏
Comrade Auwal Adam.