22/08/2019
JAGORAN MASU MAGUNGUNAN MUSULUNCI
NA DAYA (1)
NA
MAL. ABBA MAI SALATI
2018
MA'ANAR ISLAMIC CHEMIST A TAQAICE
Shi 'Islamic Chemist' kalma ce wadda ta haxa Turanci da Larabci.
'Islamic' kalma ce da take nufin Musulunci. ita kuma kalmar 'Chemist' tana nufin gurin magani.
Idan ka haxa kalmomin wato 'Islamic' da 'Chemist' zai baka ma'ana ta gurin bada magani na Musulunci.
To ka ga tun da guri ne na ba da maganin Musulunci, ya zama maganin Musulunci ya zama wanda yake wannan aiki shi wakiline na Musulunci kuma ya k**ata kafin mutum ya xau wani magani ya bayar to ya k**ata ya nemi ilimin abin. Domin Manzo (SAW) ya ce:
"Wanda ya bada magani ba tare da ilimi ba, ko me ya faru shi zai biya fansa".
Idan kuwa ka nemi sani to za ka amfana kuma zaka amfanar.
Wannan shine dalilin rubuta wannan xan littafi domin ya amfanar da kuma tunatar da mu abin da bamu sani ba. Allah Ya datar da mu, Amin.
Kma shi kansa neman magani yayin cuta ibadane, k**ar yadda Manzon Allah (SAW) yake cew:
تدور يا عباد الله فإن الله لم يضع داع إلا وضع له دواء.
Ma'ana (Ku nemi magani ya ku bayin Allah, domin Allah bai sanya wata cuta ba sai da ya sanya mata magani".
HANYOYIN GANO CUTA
Ka sani ya kai xan'uwana, cututtuka sun bambanta da juna don haka ka manninsu da alamominsu ma sun bambanta da juna, kuma kowace cutarwarta a jikin xan'adam ya bambanta da na 'yar uwarta. Masana ilimi sun kasa cutuka izuwa kashi biyu ko fiye da haka. Amma za mu xau kashi biyu wanda sune s**a fi bayyana nau'i na farko sune cutuka masu rai, nau'i na biyu sune cutuka marasa rai.
1-Cututtuka masu rai sune waxanda idan aka xau ma'auni na zamani za'a gansu suna da rai suna motsi.
2-cututtuka na biyu wato marasa rai sune cutukan ciwon suga da hawan jini a bisa misali su waxannan sinadarai ne da suke qaruwa a jikin xan'adam sai su haifar masa dasu, su kuma sinadarai ba rai ne da su ba a zahiri.
Tun da muna bayani akan qarawa juna sani za mu yi bayani akan cuta ta jiki da cuta ta ruhi (k***a), wato (علاج الروحنية).
Cutukan jiki alamominsu a zahiri suke. Za mu xau cutuka na zahiri mu yi bayani domin idan mutu ya zo gurinka da waxannan alamomi za ka gane abin da yake damunsa kuma ka san abin da zaka bashi.
ALAMOMIN CUTUTTUKA DA MAGANINSU:
1-Hawan Jini; Alama ta farko:
1-Yawan ciwon kai.
2-Kasa bacci.
3-Gani dusu-dusu.
4-Ciwon qafa.
5-Damuwa da saqe-saqe a zuciya.
6-Jin nauyin jiki vari xaya.
Waxannan sune kaxan daga cikin alamomin hawan jini. Amma kuma ba wai daga ka ji mutum da waxannan alamomi ka tabbatar masa cewa yana da wannan cuta. Ya k**ata ka samu kayan gwaje-gwaje na zamani ko ka samu wani qwararre da zai gwada don tabbatar da cutar saboda baiwa mutum maganin hawan jini ba tare da cewar yana da shi ba, wannan matsalace. Haka kuma ya ke ga kowacce cuta.
MAGANI:
Da farko za ka umarci mara lafiya wato mai hawan jini da ya dinga fita yana motsa jiki, sannan ya rage cin gishiri da kafi zabo, ko ya ma daina gaba xaya. Ya kuma guji shiga abin da zai tayar masa da hankali ko jawo masa rigima.
MAGANIN KAUTAR DA HAWAN JINI:
1-Farin zovorodo rabin gwangwani.
2-Tafarnuwa qwallo uku.
3-Tasiri kwalba xaya.
4-Zuma madaidaiciya.
Sai a tafasa su da safe a ringa sha kaxan kaxan har zuwa yamma, a yi haka zuwa tsawon kwana bakwai, za ka manta da kana da hawan jini InSha Allah.
2-CIWON SUGAR:
Kaxan daga cikin alamominsa:
1-Yawan fitsari musamman da dare.
2-Yawan shan ruwa.
3-Ramewa.
4-Bushewar maqogwaro.
5-Raunin Mazakuta.
6-Qin warkewar ciwo da wuri.
7-Yawan gumi.
Idan mara lafiya ya faxa maka waxannan alamomi to shi yake nuna yana da cutar sugar sai ka turashi wajen gwaji don tabbatarwa. Da zarar an tabbatar to ka ga kana da mak**a, don da yawa za ka ga alamomi amma ba ciwon bane, qila za ka ga alamomin kamuwa ne wanda da zarar ya rage amfani da abubuwan da suke xauke da s**ari to sai cutar ta koma baya.
MAGANI:
Babban maganin ciwon sugar shine dai na shan duk abin da yake xauke nau'in s**ari ko masu sa qiba, kuma ya tambayi masana irin abincin da ya dace mutum ya ci, kuma a nan gaba za muyi bayanin daga nau'in abincin da ya dace mai sugar ya riqa ci.
MAGANIN CIWON SUGAR
1-Garin yaxiya gwangwani xaya.
2-Shuwaka rabin gwangwani.
3-Kashe zaqi rabin gwangwani.
4-Gemun masara rabin gwangwani.
Sai a dakesu ya dinga shan rabin cokali safe da rana da dare, za ka manta da ciwon Insha Allahu. Kuma ya guji abin da zai ji masa ciwo musamman a qafa.
TAIFOD DA MALERIYA
Ita cutar Taifod da Maleriya haqiqa cuta ce, mai sarqaqiya domin kuwa wannan cuta tana iya rikita ma'abocinta ta inda take iya rikita shi ya riqa surutai wasu lokuta, k**ar mai aljanu. Haqiqa wasu lokuta hakanne yake faruwa idan an je wajen masu bada magani sai su bada maganin aljani wanda shi kuma ba zai yi aiki a kan wannan cutaba.
Don haka yana da kyau a duk lokacin da mara lafiya ya zo maka to ka tsaya ka fahimci irin abubuwan da zai gaya maka da yake ji idan ka ji abin yana da alaqa da wannan cuta to sai ka tabbatar da irin maganin da za ka bayar don samun sauqi ko warakar Insha Allah.
ALAMOMIN TAIFOD DA MALERIYA
Yana daga cikin alamomin cutar Taifod da maleriya k**ar haka;
1-Yawan ciwon kai.
2-Zazzavi mai naci.
3-Kasala da Ramewa.
MAGANI:
1-Lemon tsami.
2-Xorawar Turawa.
3-Tafarnuwa.
4-Tazargade.
5-Jan Gauta.
Sai a dafasu da ruwa kofi shidda a ringa shan kofi xaya da safe xaya da rana xaya da dare. InSha Allahu, za a samu waraka.
BASIR:
Basir yana xaya daga cikin lalurar dake shafar auratayya, haqiqa basir yana da salo iri-iri wanda wani lokaci sai a rasa abin da yake damun mutum. basir cuta ce wadda bata bar tsoho ko tsohuwa ba, kuma bata bar babba ko yaro ba, matashi ko matashiya, don haka maganinsa iri-irene, wanda ya dace da kai kawai za ka riqe, wani lokaci sai kai ta shan maganin ka ji shiru, to kada ka ce zaka daina ka gaji da karvar magani, ka cigaba za ka dace Insha Allah.
Basir in yai qarfi ya kan hana xa namiji kuzari, sannan ga mace ya kan iya xauke ni'imarta.
ALAMOMIN BASIR:
1-Basir kalma ce ta Larabci, Hausawa na kiransa xan kanoma, da yawa bahaushe na xaukar duk cutar da ta cushe masa ciki da basur, da yawa akwai cutuka masu k**a da basur amma bashi bane, domin yana da abubuwa masu k**anceceniya da shi k**ar yadda muka faxa, k**ar mutum ne ya ga damo, qadangare, guza, ka ga suna da k**anceceniya amma kowanne jinsinsa daban, shi ma basir aka ne.
MAGANI:
Wanda basir yake takura masa ya nemi:-
1-Marke.
2-Lemon tsami rabi.
3-Tafarnuwa.
4-Barkono tsiduh qwaya 3.
5-Jar kanwa kaxan.
A tafasa a dinga sha za'a samu waraka Insha-Allah.
Ko a nemi:
1-Sabulun sha xan Sakkwato.
2-Ruwan Abarba.
3-Garin Hannu.
4-Lemon tsami.
5-Vawon lemon zaqi.
6-Jar kanwa kaxan.
Sai a jiqa su tsumu a dinga tsiyaya ana sha, Insha Allah ko da mai sa qugin cikine, zaka manta da basir.
Ku sani maganin basir karva-karvane shi ya sa muka ce idan ka sha wani bai yi ba, to kar ka karaya ka cigaba da jarraba wani za ka samu wanda zai karveka, Insha Allah.
Akwai maganin basir mai suna mai Vaure yana taimakawa mutum da basir yake hana shi kuzari wajen iyali da izinin Allah.
SANYI:
Sanyi mashahuriyar cuta ce don haka da yawa masu magani sunai wa sanyi sharri duk da cewa shine asalin kowacce cuta, k**ar yadda Manzo (SAW) ya ce: أصل كل داء البرد
"Asalin wasu cututtuka daga sanyi ne".
Da yawa masu magani idan cuta ta gagaresu sai su ce sanyi ne, amma da yawa ana dacewa da yawa kuma ana samun akasin haka.
KASHE-KASHEN SANYI
1-Kashi na farko: Sanyi Baridi.
2-Kashi na biyu: Sanyi Harri.
3-Kashi na uku: Sanyi Yabisi.
4-Kashi na huxu: Sanyi Raxubi.
SANYI BARIDI (Mai sanyi)
Wannan ana xaukarsa lokacin canzawar yanayi, lokacin da ake hunturu.
ILLOLINSA:
1-Yana sa mura.
2-Fitar da majina.
3-Bushewar fata.
4-tsagewar Leve.
Ka sani kowane sanyi ana yi masa magani irin nasa, sai a samu lafiya.
MAGANI:
1-Yawaita shan rake.
2-Idan ya zamana ya yiwa mutum illa ana so a rabu da shi anemi;
1-Man Na'a-na'a kwalba xaya.
2-Man tafarnuwa kwalba xaya.
3-Man zogale kwalba xaya.
Sai ka haxesu guri xaya, kana shafawa a jiki da kuma cinsa a abinci, kuma mutum ya guji wanka da ruwan sanyi, domin lokacin ne Asma take tahi.
Ko ka nemi wani magani namu mai suna "Sanya" ko kuma "Tasiri" suna taimakawa a wannan va***re.
SANYI HARRI (MAI ZAFI)
Shi wannan ana xaukarsa a kudu ko inda ake noma ko mai wanki, lokacin da yake shigarka baka jinsa har sai ya gama shigarka.
HANYOYIN DA AKE SAMUNSA:
1-Zama a guri mai danshi.
2-Zaman kudu da garurruka masu teku.
3-Aikin Rafi ko noma.
4-Wanki ko kamun kifi.
5-Yawan shan abu mai sanyi.
6-Ko yawan amfani da kayan sanyo, ta nan ake samunsa.
ALAMOMINSA:
1-Riqewar gava.
2-Ciwon jiki.
3-Fitowar quraje.
4-Tanqwarewar gava.
5-Kasa tafiya.
6-Zazzafan jiki.
7-Ciwon baya da ciwon qashi.
ILLOLIN DA YAKEWA JIKI:
1-Tsaida bugun zuciya.
2-Ruguza tsarin jiki
3-Lalata tsarin kayan ciki da toshe qofofin da abinci yake bi.
4-Xaukewar qarfin jiki.
5-Busar da fatar jiki.
6-Ciwon maqogwaro da lalata tsarin murya.
MAGANI:
1-Garin Habbatus-Sauda gwangani xaya.
2-Garin Hulba gwangwani xaya.
3-Garin tafasa rabin gwangwani.
4-Barkono gwangwani uku.
Sai a haxesu a mayar k**ar yaji sai a ringa ci a abinci. Za'a warke da yardar Allah.
SANYI YABISI (Busasshen Sanyi)
Shi wannan sanyi ya fi k**a mata su kuma mata sai su ba maza su kuma inda s**ai fitsari sai wani ya xauka shi ake kira da "Infection" da turanci.
Shi da yawa mace tana xaukarsa a ban xaki, shi farjin mace kodayaushe yana da danshi domin hana cutuka shiga. Allah Ya halicci wasu sinadarai a ciki masu hana kamuwa da cututtuka ana kiransu "Candidiasis" da turanci. Da zarar mai fama da wannan cutar tayi fitsari sai 'yar uwarta wadda ba ta da wannan sinadarai ta xauka daga nan sai ya fara haifar mata da qaiqayin gaba.
ALAMOMINSA:
Qaiqayin gaba.
Fitar farin ruwa.
Xaukewar sha'awa.
Jin zafi yayin saduwa.
Rashin jin daxi yayin mu'amalar aure.
Bushewar gaba.
Xaukewar ni'ima.
Ko da kin sha maganin ni'ima ke ba zai miki ba, saboda sanyi ne yake cinye sinadaran maganin za ki ji ana baki labarin magani amma ke in kin sha ba zai miki magani ba.
MAGANI:
A nemi magani mai suna "Jaura" sannan ki yawaita amfani da ruwan zafi kuma duk fant xin da kika yi amfani da shi ki wanke da gishiri da detol kafin ki mayar da shi.
SANYI RAXUBI (Xanyen Sanyi)
Shi wannan yafi takurawa maza, domin yana qanqantar da gaba ya xauke sha'awa.
HANYOYIN XAUKARSA:
Wasa da gaba har sai an yi inzali.
Goga sabulu har sai an yi inzali.
Qin yin aure da wuri har maniyin mutum ya ruve.
Takure sha'awa ba tare da biyan buqata ba.
ILLOLIN DA YAKE YI:
Mutuwar gaba.
Qanqancewar gaba.
Saurin kawowa.
Wahalar kawowa.
Qaiqayin kwarkwaron gaba.
Ciwon gaba.
Fitar farin ruwa.
In yai nisa ana iya samun waxannan alamomi har ya kai ga kashe qwayoyin haihuwa.
MAGANI:
Mun tanaji wani mashahurin magani akan wannan matsala. Domin wannan matsala hantsice leqa gidan kowa, su kuma mata mazajensu basa gamsar da su, amma basa iya gaya musu.
Wannan magani shine "Nisan Dare" qarfin maza yana taimakawa maza akan matsalolin aurataya, za ka warke lokaci qalilan insha Allahu.
HANYOYIN GANO CUTA TA BAYANIN MARA LAFIYA DA SIFFOFINSA
Da zarar an kawo maka mara lafiya za ka kalli idanunsa yayin da kaga yayi kore shar, shi yake nuna cewa alama ce ta ciwon hanta.
Ciwon gadon baya (qugu) alama ce ta ciwon qoda.
Haki yayi shiga qura ko hayaqi alama ce ta ciwon Asma.
Kumburin jiki da hannaye alama ce ta ciwon zuciya.
Saurin jin yunwa da murxawar ciki alamace ta ciwon Olsa.
Zazzavi mara xaukewa mai zafi alama ce ta ciwon Taifod.
Zazzavi mai kaiwa da komowa musamman da magriba alama ce ta ciwon maleriya.
Waxannan alamomi da muka bayyana ba shine yake nuna cewa da ka ga mutum da xaya daga cikinsu ya kamu da wannan cutaba, sai ka tuntuvi masana domin yanzu an yo abubuwa na zamani dan gano cututtuka, wannan mun yi a taqaice ne don taimakawa.
NISAN DARE (QARFIN MAZA):
Wannan maganin shahararren magani ne na qarfin maza yana qara kauri da kuma hana saurin kawowa yana sa mutum ya daxe yana gamsar da iyalinsa yana kuma wanke mara.
Yana maganin sanyi yana kuma qara ruwan maniyyi.
Yadda ake amfani da shi ana shansa da ruwan shayi babu madara ana juyeshi duka sachet.
Ana shansa kafin a kwanta da minti (20) wanda kuma baya iya jima'i sau uku (3) a rana, yana iya amfani da shi a ko yaushe.
Allah Ya sa mu dace. Amin.
ALAMUN RASHIN HAIHUWA NA VANGAREN SANYI SUNE:
Fitar farin ruwa ta gaba. *Qaiqayin jiki da na farji.
Yawon wani abu k**ar tana.
Ciwon qirji, baya, zafin jiki da sauransu.
MAGANI:
A nemo saiwar zogale guda (7).
Tafarnuwa guda tara (9) a haxa da garin hano a tafasa ta dinga shan kofi xaya sau uku a rana. sannan ta dinga yawan shan kwallon tafarnuwa da ma'ul-miyahi sau uku a kullum zata samu ciki a cikin wata uku insha Allah.
MAGANIN ALJANI
Idan akai magani aljani yaqi fita sai a samu sabulun dawa'u sabuni da duhunul – jinni a dinga cakuxasu ana wanka dasu sannan a dinga turare da madafa'ush-sharri in bai fita ba zai qone.
FA'IDAR DAWA'US SABUNI:
Wannan sabulu yana da fa'idoji k**ar haka:-
Wanda dashi na lalata sihiri. - Kuma yana qona aljani.
Aljani ba zai cutar da kaiba in kuma wanka dashi.
Yana lalata mahassada da abokan gaba.
Yana maganin kwantaccen ciki da sauransu.