21/03/2025
ZIYARAR BARKA DA SHAN RUWA.
Mai Girma Babban Kwamishinan Hukumar Ƙidayar Yawan Al'umma Da Gidaje Na Tarayyar Nigeria Mai Kula Da Jihar Kano, Hon Dr Aminu Ibrahim Tsanyawa Ya Kai Ziyarar Barka Da Shan Ruwa Gidan Alkur'ani Kano Dake Unguwar Tudun Yola GRA, Gidansu Hon Abba Rabee'u S.A Youth Mobilization A Daren Wannan Rana, Inda Aka Shirya Shan Ruwa Na Musamman Tare Da Gabatar Da Addua Ga Mai Girma Babban Kwamishina.
Anyi Jawabai Da Yawa Kuma An Godewa Mai Girma Kwamishia Abisa Ayyukan Alheri Da Ya Gudanar Musamman A Ma'aikatar Lafiya Wadda Dumbin Al'umma S**a Amfana, Tare Da Fatan Zai Ninka Himma Da Kokari K**ar Yanda Ya Saba Abisa Wannan Sabon Office Daya Samu.
Acikin Jawabinsa Khalipha Alhaji Almustapha Rabiu Yayi Addua Akan Allah Yayi Jagora Ya Biya Bukata Yasa Agama Lafiya.
A Karshe Mai Girma Kwamishia Ya Damqa Takardar K**a Aiki Ga Hon Abba Rabee'u A Matsayin Mataimaki Na Musamman Akan Harkar Tattara Matasa. (S.A YOUTH MOBILIZATION)
Mai Girma Kwamishia Ya Samu Rakiyar Alhaji Ahmad Tatsan, Tare Da Sani Aminu Tsanyawa, Salisu Ibrahim Yahaya Da Sauran Masoya.
Muna Godiya Kwarai Da Gaske, Abisa Wannan Zumunci Da Karamci, Allah Ya Huta Gajiya.
Dr Nura Dahiru Kademi
Sakataren Yada Labarai
21/ Maris 2025