13/11/2025
MEKE JAWO ZUBAN YAWU YAYIN DA MUTUM YAKE BACCI?
Zuban yawu yayin da mutum yake bacci (drooling ko hypersalivation) yana faruwa ne sakamakon yanayin kwanciya (ko wasu matsaloli) wanda hakan ke tunkuɗo yawu daga cikin baki zuwa waje.
Idan kana fama da wannar matsalar ka ziyarci likita.
👉 ABUBUWAN DAKE HAIFAR DA MATSALAR 👇
1- Kwanciyar gefe ko kwanciyar akan ciki
2- Toshewar hanci sakamakon mura wanda zaisa mutum yadinga shaƙar iska ta baki
3- Taruwar sinadarin acid a ciki, dawowar abinci zuwa maƙwogoro {Gastrointestinal reflex disorder (GERD)} wanda ke haifar da taruwan yawu a baki
4- Shan wasu ƙwayoyin magani na Antibiotics ko wasu cutuka daban
5- Haɗiya daƙyar (Dysphagia)
6- Ciwon bacci na "Apnea"
7- Sanyi (infection) a maƙwoshi (epiglottitis) kamar agalawa wanda yake jawo kumburi da wahalar haɗiya.
8- Cututtukan da s**a shafi ƙwoƙwalwa wanda suke illa ga jijiyoyi da tsokokin da suke kula da haɗiya da baki kamar cutar shanyewar ɓarin jiki.
👉 HANYOYIN KARIYA 👇
1- Kwanciya a kan baya
2- Shan ruwa dayawa
3- Sha ko tsotsan kayan itatuwa masu tsami
4- Nisantar shan abu mai zaƙi lokacin kwanciya
5- Amfani da Mandibular device
6- Shan maganin da zaiyi daidaita sinadarin Acid dake ciki.
📝 Zauren Abu Muhaisin Islamic and Traditional Herbal and Marriage Counselling.