FUAD ISLAMIC MEDICINE MISAU

FUAD ISLAMIC MEDICINE MISAU WANNAN SHAFIN ZAI RINKA KAWO MUKU MAGUNGUNAN MUSULUNCI BISA KOYARWAR MANZON ALLAH SALLALLAHU ALAIHI WA SALLAM BISA FAHIMTAR MAGABATA NA KWARAI INSHA ALLAH.

WANNAN PAGE DIN ZAI RINKA KAWO MUKU, BAYANAI AKAN MAGUNGUNAN MUSULUNCI MASU INGANCI WADANDA S**A TABBATA A SUNNAH BISA FAHIMTAR MAGABATA NA KWARAI INSHA ALLAH! DON KARIN BAYANI ZA A IYA TUNTUBAR MU DA INBOX KO TA LAYIN WAYAR MU INSHA ALLAHU. MUN GODE. ALLAH YA MANA DA CE.

Ku yi ƙoƙarin ku mallaki wannan maganin, musamman don yin azumi ba tare da wata matsala ba a watan RAMALANA in Sha Allah...
15/02/2026

Ku yi ƙoƙarin ku mallaki wannan maganin, musamman don yin azumi ba tare da wata matsala ba a watan RAMALANA in Sha Allah.

09031562132

10/02/2026
FA’IDOJIN MAGUNGUNA*ALBABUNAJ*Yana sauƙaƙa matsalolin zuwan jinin al’ada, da radadin da ke zuwa tare da shi. Yana taimak...
03/02/2026

FA’IDOJIN MAGUNGUNA

*ALBABUNAJ*

Yana sauƙaƙa matsalolin zuwan jinin al’ada, da radadin da ke zuwa tare da shi.

Yana taimakawa wajen rage hawan jini (Hypertension) da kare zuciya daga matsalolin da hawan jini ke haifarwa.

Yana rage ciwon kai mai tsanani ko jujjuyawa, musamman wanda hawan jini ke haddasawa.

Yana magance ciwon baki, ana sha ana kuma kuskura da shi.

Yana bada nishaɗi, yana kuma taimakawa wajen samun barci mai daɗi.

Ana amfani da shi wajen magance sanyi, mura, da dushewar murya.

🫖 Yadda ake amfani da shi:

Ana yin shayin Albabunaj, a sha da ɗumi-ɗumi safe da yamma.

MUNA DA ASALIN ALBABUNAJ ƊIN GA MAI BUƘATA.

⊙ FUAD ISLAMIC HERBAL MEDICINE

📍 Misau, Bauchi State

📞 0903 156 2132

01/02/2026
DOMIN RAGE TUMBI, KITSE DA ƘIBAAna samun taimako ta hanyar magunguna idan aka yi amfani da su yadda ya dace, da izinin A...
29/01/2026

DOMIN RAGE TUMBI, KITSE DA ƘIBA

Ana samun taimako ta hanyar magunguna idan aka yi amfani da su yadda ya dace, da izinin Allah.

*MAGUNGUNAN DA AKE AMFANI DA SU:*

• Iklil Jabal
• Si’itir

Ana haɗa su a yi shayi, a sha.

Suna taimakawa wajen rage kitse mai cutarwa (cholesterol) da kuma tumbi, ba tare da illa ga mai amfani ba idan an yi amfani da su yadda ya dace.

*DOMIN RAGE ƘIBA:*

Ana iya haɗa waɗannan:

Citta
Green Tea
Khal Tuffa
Ganyen Na’anaa

A yi shayi da su, a sha akai-akai, suna taimakawa wajen rage ƙiba.

*WANI HANYA MAI SAUƘI:*

Idan aka haɗa:

Lemun tsami
Na’anaa
Khal Tuffa

A yi shayinsu, suna taimakawa wajen:
Rage cholesterol
Rage tumbi

KAMMUN (Cumin):
Bisa binciken likitocin Musulunci, idan aka yi shayin kammun aka sha:

Yana rage kitse mai cutarwa.
Ba ya da cutarwa ga mai amfani.

Domin duk abin da Allah Ya halitta a jikin ɗan Adam yana da amfani, sai dai yawaitarsa na iya zama matsala.

📞 DOMIN ƘARIN BAYANI & TUNTUƁA:

WhatsApp / Kira:

📱 09031562132
📱 08067676223

Dafatan Allah Ya ba mu dacewa, Ameen.

FUAD ISLAMIC MEDICINE MISAU

*KANA SON SAMUN KAIFIN BASIRA *Shin ko kana karatu kana mantawa nan take ?Ko yawan confusion ne matsalar ka ?Ko kana fam...
28/01/2026

*KANA SON SAMUN KAIFIN BASIRA *

Shin ko kana karatu kana mantawa nan take ?

Ko yawan confusion ne matsalar ka ?

Ko kana fama da nauyin ƙwaƙwalwa ?

Ko rashin Maida hankali ga abu Mai muhimmanci ?

Shin ƙwaƙwalwar ka na dushewa ?

Ko kana tafiya kai kaɗai kana magana da kanka kana dariya ?

Ko kana buƙatar daidaita tunaninka ?

Ka Sha wannan maganin kwatan ƙaramin cokali ayi shayi da shi, asha da zuma da madara.

Bayan Wata Ɗaya zaka tabbatar ashe brain ɗinka na Neman taimako.

Tuni ƴan uwa s**a yi amfani da wannan maganin s**a samu lafiya da izinin Allah.

Masu buƙatar wannan maganin a neme mu ta WhatsApp:

+2349031562132

FUAD ISLAMIC MEDICINE MISAU

*KO KA SAN GANYEN KARAS NA DA AMFANI FIYE DA KARAS ƊIN KANSA?!!*✔ Yana ƙara garkuwar jiki✔ Yana tsaftace jini da hanta.✔...
27/01/2026

*KO KA SAN GANYEN KARAS NA DA AMFANI FIYE DA KARAS ƊIN KANSA?!!*

✔ Yana ƙara garkuwar jiki

✔ Yana tsaftace jini da hanta.

✔ Yana taimakawa wajen narkewar abinci.

✔ Yana ƙarfafa ƙashi da zuciya.

✔ Yana inganta lafiyar fata da gashi.

Kar ka zubar da ganyen karas!

Akwai abubuwan masu amfani na lafiya da Allah Ya saka a cikinsa.

Ana iya tafasawa a sha, ko a haɗa da abinci.

FUAD ISLAMIC MEDICINE MISAU

0903 156 2132

IDAN KANA JIN WADANNAN ALAMOMI, TO KA IYA SAMUN APPENDICITIS (APPENDIX)Yawancin mutane na kiransa “Appendix”, amma a asi...
26/01/2026

IDAN KANA JIN WADANNAN ALAMOMI, TO KA IYA SAMUN APPENDICITIS (APPENDIX)

Yawancin mutane na kiransa “Appendix”, amma a asibiti ana ce masa Appendicitis.

1. Ciwon ciki;

Yana farawa ne a tsakiya ko kusa da cibiya.

Daga baya yana komawa ƙasan dama na ciki.

Ciwon yana ƙaruwa idan:

Aka yi tari.

Aka yi tafiya.

Aka matsa ciki.

2. Rashin son cin abinci:

Abinci baya yi wa mutum daɗi kwata-kwata.

3. Amai ko tashin zuciya:

Yakan zo ne bayan ciwon ciki ya fara.

4. Zazzaɓi;

Yakan fara kaɗan, daga baya ya ƙaru.

5. Kumburin ciki ko taurin ciki:

Musamman idan aka matsa, ciwon yana tsananta.

6. Canjin bayan gida:

Gudawa ko rashin bayan gida
Ko iska bata fita.

7. Jin kasala sosai:

Jiki yana yin rauni da gajiya.

GARGADI:

Duk wanda ya ji waɗannan alamomi kada ya tsaya waje a masa gwaji na Appendicitis saboda a ba shi magani na gaggawa, domin idan ya fashe yana iya zama barazana ga rai.

Allah Ya ba da lafiya.

FUAD ISLAMIC MEDICINE MISAU

+2348067676223
0903 156 2132

23/01/2026

MAGANIN CIWON CIKI KOWANE IRI.

FUAD ISLAMIC HERBAL MEDICINE MISAU

No 2. Tamsuguri Turaki Street Misau.

+2348067676223
+2349031562132

*HUMAN PAPILLOMAVIRUS (HPV)*HPV cuta ce da ake iya kamuwa da ita ta hanyar hulɗar fata da fata, musamman ta jima’i.Tana ...
21/01/2026

*HUMAN PAPILLOMAVIRUS (HPV)*

HPV cuta ce da ake iya kamuwa da ita ta hanyar hulɗar fata da fata, musamman ta jima’i.

Tana iya haifar da ƙuraje ko tsiro-tsiro a gaɓoɓin jima’i (mazuƙuta) na maza da mata.

ALAMOMI:

Ƙuraje ko tsiro-tsiro a gaɓoɓin jima’i.

Wani lokacin kuma yana kasancewa ba tare da ciwo ba.

Wasu nau’ikan na iya ɓoya na dogon lokaci.

*MAGANI:*

A asibitoci, ba dukkan nau’ikan HPV ke da magani kai tsaye ba, sai dai ana kula da alamominta.

Amma a magungunan Islama na gida, akwai hanyoyin magani da ake amfani da su tare da kulawar masana.

*GARGADI:*

Duk mai fama da irin wannan matsala ya tuntuɓi masana lafiya ko ƙwararru kafin fara amfani da kowace hanya ta magani.

FUAD ISLAMIC MEDICINE MISAU

+2348067676223

+2349031562132

No 2. Tamsuguri Turaki Street Misau.

FA’IDADOJIN MAGUNGUNADaga Cibiyar Fuad Islamic Medicine Misau.1. ƘIRIFAT:Kirifat wani bawone na bayan icce wanda yake ƙu...
20/01/2026

FA’IDADOJIN MAGUNGUNA

Daga Cibiyar Fuad Islamic Medicine Misau.

1. ƘIRIFAT:

Kirifat wani bawone na bayan icce wanda yake ƙunshe da sinadarai masu gina jikin ɗan Adam da kuma kariya daga garkuwar jiki.

Ɓawon kirifat yana da ƙamshi ga kuma kasancewarsa da daɗin ɗandɗano yayin da ka sanya shi a baki, ko shakka babu da zaran ka sanya shi a bakin ka ka taunashi zakaji shi yana da kaifi.

Yana daga cikin magungunan da yakeyi kamar magance;

Cutar basir, maganin Aljanu, hawan jini, sihiri, ciwon kai, magance damuwa da yawan shakku, ciwon ƙirji, asma, ciwon ciki, da sauransu.

GA YADDA AKE HAƊA MAGANIN:-

1) Ana cin wannan bawon na ƘIRIFAT idan an tsotse ɗanɗanon a tofar da tsakin domin magance cutar damuwa da yawan shakku, tare da dai-dai ta hawan jini, da kuma magance matsalar Aljanu.

2) Ana yin turarensa bayan an jiƙa shi da man Habbatus Sauda domin magance farfaɗiya da sihiri da kuma Aljannu, musamman waɗanda s**a buge ya faɗi.

3) Ana daka shi a haɗa da zuma da H/sauda domin maganin cututtukan da aka rasa kansu.

4) Ana tafasa shi da garin Yanson (Kammun) sannan a zuba zuma asha kamar shayi domin magance ciwon kai, basur, cutar sihiri, ciwon ciki, ciwon ƙirji da kuma ciwon asma (amma idan ciwon asma akeso a magance sai an haɗa da garin Shajratu Maryam).

FUAD ISLAMIC MEDICINE MISAU
No 2. Tamsuguri Turaki Street Misau, Bauchi State Nigeria.
08067676223 ko 09031562132

Address

Misau

Opening Hours

Monday 08:00 - 22:00
Tuesday 09:00 - 22:00
Wednesday 09:00 - 22:00
Thursday 09:00 - 22:00
Friday 09:00 - 22:00
Saturday 08:00 - 22:00
Sunday 08:00 - 22:00

Telephone

+2349031562132

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when FUAD ISLAMIC MEDICINE MISAU posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Practice

Send a message to FUAD ISLAMIC MEDICINE MISAU:

Share

Share on Facebook Share on Twitter Share on LinkedIn
Share on Pinterest Share on Reddit Share via Email
Share on WhatsApp Share on Instagram Share on Telegram

Category