Apc Gombe & Bauchi State Forum

Apc Gombe & Bauchi State Forum NO ONE IS PERFECT THAT'S WHY PENCILS HAVE ERASER

Permanently closed.
12/04/2019

☸☸☸☸☸☸☸☸☸☸☸☸
*🌐DUNIYA MAKARANTA KASHI NA BIYU (2)🌐*

*Rubutawa: Dr. Muhammad Mansur Sokoto*

👉366. Abu biyu ba su dorewa: Karfi da Kuruciya. Abu biyu ba su bacewa: Alheri da Zumunta.

👉367. Gara karewar lokaci da bata lokaci. Idan lokacinka ya kare za ka mutu. Mutuwa tana yanke ka ne daga duniya da abin da ke cikin ta. Bata lokaci kuwa yana yanke ne daga Allah, da jin dadin bautar sa.

👉368. Duk abu mai daraja yana da mayafi. Alqur’ani yana da makari. Alqalami yana da marufi. Takobi yana da kube. Alawa tana cikin takarda. Lemu da Ayaba, Abarba da Gwadda. Kai, duk abin kwarai ana yi masa sutura. Lulluvi adon matan kirki

👉369. Idan kana son duniya ka yi karatu. Idan kana son lahira ka yi karatu. Idan kana son duniya da lahira ka yi karatu, sannan ka yi aiki da karatu.

👉370. Alqur’ani shi ne daminar zukata. Idan ka ga ana karanta Alqur’ani ba ka jin wani tasiri a zuciyarka to ka yi kabbara hudu ga zuciyarka. Ta riga ta mutu

⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇
Email: jibwissocialmediaktlg@gmail.com
Facebook: Jibwis Katsina L.G
WhatsApp: 07062584992, 08038977817, 08034453678, 08036958490

13/03/2019

السلام عليكم ورحمة الله وبركا ته

*Ana мυѕlιм*
*__انا مسلم____________*

” بسم الله الرحمن الرحيم
*______________________*

*HUKUNCE-HUKUNCEN 'RANTSUWA' A MUSULUNCI !*

_Darasi Na 2_

Karkasuwar Rantsuwa : Anan malamai s**an karkasa rantuwa zuwa kashi-kashi, zamu ambaci kashi uku da hukunce-hukuncensu daga cikin kasha-kashan rantsuwar domin galibi wadannan ukun su mukafi cudanya da su lokacin yin rantsuwa Allah ya bamu sa'a amin.
Kashi Na Farko: Rantsuwar wargi. Wannan ita ce rantsuwar da malai suke kiran ta Yaminul-Laghwi. Malaman sun karawa juna sani wurin me ake nufi da Rantsuwar wargi ko yasasshiyar Rantsuwa? Wasu s**a ce :Ita ce irin rantsuwar dake guda a bakuna ba tare da angudurta nufin rantsuwar a zuciya ba, k**ar: Wallahi ba haka bane, ko Wallahi haka ne. wasu kuma s**a ce ita ce: rantsuwar da mutum ya kan yi akan tabbas abinda ya rantse a kan shi daidai ne sai daga baya abin ya bayyana ba haka bane, misali: ka hango wani mutum daga nesa sai ka rantse da Allah waccan mutumin wane ne, domin ka kalli tsawon shi da tafiyar shi da komai na shi, sai bayan ya matso kusa sai ya bayyana ba shi dinne ba, wannan ko yakan auku sosai(akwai lokacin da naje sakkwato zuwa na nafarko kenan akaita maraba da ni ana cewa Aliyu ka zaka sai nake ta mamaki ashe a inda na sauka din akwai wani ya yi tafiya shima sunan shi Aliyu wai mun yi k**a sosai) wadannan nau'uka biya na rantsuwa mukan sami kammu a ciki kwarai da gaske, to irin wannan rantsuwar tana da Kaffara? Irin wannan rantsuwar bata da wata kaffara domin Allah bai k**a wanda ya yi ta da laifi k**ar yadda Allah ya ke cewa "Allah ba ya k**a ku da laifi saboda yasasshiyar rantsuwowin ku." Suratul-Bakara, aya ta :225. (wato rantsuwar wargi) k**ar yadda bayanin ta ya gabata.
Kashi Na biyu :Rantsuwa mai halakarwa. Wannan kashi na biyu da zamu yi bayanin shi yanzu shi ne malamai suke kiran shi Al-Yaminul-Ghamus, wato rantsuwa me halakarwa. Wannan ita ce: Rantsuwar da mutum zai yi ta akan karya domin cin hakkin wani. Wannan zai nuna mana dukkan wata rantsuwa akan karya da mutum zai yi domin ai anfani da wannan rantsuwar a bashi hakkin wani ko aba wani hakkin wani ita ce ake Magana a yanzu, misali:Mutum ne yake so ya dirkake fegin wani ko gona koma dai menene ya tsaya tsayin-daka da rantsuwa domin a bashi wannan fegen ko wannar gonar, ko kuma ya kira wani ya rantse a matsayin sheda domin a bashi shi kuma wanin ya rantse. To me nene hukuncin haka? Abinda ya k**ata a sani dukkan wani hukunci da alkali ya yanke a kotu baya halatta haram ko ya haramta halal, saboda haka idan alkali ya yi iyakar binciken shi ya zamana abinda ya binciko shi ne wannan fegi naka ne alhali ba naka bane kotu ta dauka ta baka akan abinda ta dogara da shi na shaidu to wannan hukunci baya halatta wannan fegi a wurin Allah wanda yake masanin boye da sarari. Abu na biyu kuma irin wannan rantsuwa ba'a mata kaffara domin ta wuce haka bala'inta ya kai bala'I, ita dai kan sai idan mutum ya tuba yayi nadama ya kuma ci gaba da neman gafara wurin Allah ya kuma yi niyyar ba zai sake aikata wannan mummunan aiki ba ya kuma mayarwa me kaya kayan shi ya kuma ci gaba da istigfari muna fatan Allah ya yafe mishi, amma irin wannan rantsuwa ai ba maganar kaffara dirkashi! Ah, idan kaffara kawai zata biya ba sai mutum ya kamfato makudan kudi ba ya zo ya rantse in an bashi ya je ya dauki abinda bai kai dubu goma ba ya yi kaffara da su shikenan ya sha. Saboda irin girman da wannan rantsuwar take da shi Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabba a gare shi ya ke cewa "Dukkan wanda ya yanki hakkin wani mutum musulmi da rantsuwar shi to hakika Allah ya wajabta mishi wuta kuma ya haramta mishi Aljanna" Muslim ya ruwaito shi, kallaci irin narkon azabar da Ma'aikin Allah ya yi bayanin ta cikin wannan hadisin ka kuma kalli yadda ake fafutukar aga antara koma ta halin kaka ne Allah ya sawwake, abin la'akari anan shi ne da Ma'aikin Allah ya :'Hakkin mutum musulmi' ba ana nufin na wanda ba musulmi ba ya halatta a'a na dai musulmi shi ne bala'in ya fi, Allah ya kare mu da kariyar shi amnin summa amin summa amin.
Kashi Na uku ; Rantsuwar da ake wa Kaffara. Wannan ita ce malamai suke kira; Yaminul-Kaffara wato rantsuwar da idan mutum ya warware ta (wato karya ta) zai yi kaffara, wannan ita ce dukkan rantsuwar da mutum ya yi da Allah akan zai ai kata abu kaza sai kuma ya fasa aikatawa, ko ya rantse ba zai aikata ba sai kuma daga baya ya zo ya aikata. Sai dai malamai suna anbaton sharudda uku kafin hakan, sharadi na farko ya zama ya kudurce rantsuwar azuciyar shi ya yi niyya kenan, domin idan ba haka ba ta zama ya sasshiyar rantsuwa ke nan wacce bayanin ta ya gabata wacce ba za ai mata kaffara ba, sharadi na biyu ya zama alokacin yin rantsuwar baice 'In Allah ya yarda ba' domin idan ya ce In Allah ya yarda kuma ya fadi hakan ne har zuci ba iya fatar baki ba sannan bai sami damar aiwatar da abinda ya yi rantsuwa akan shi ba wannan ma ba wata kaffara akan shi, sai dai k**ar yadda aka ambata ya zamana ya ce hakan harzuciyar shi ba kawai mutum ya fadi iya fatar baki ba. sharadi na uku ya zama ya hada rantsuwar da In Allah ya yarda (wato In sha Allah) amma idan sai da ya yi rantsuwar sannan daga baya ya ce in Allah ya yarda to wannan bazata kange shi daga kaffara ba idan ya warware rantsuwar. Wadanan su ne sharuddan da malamai suke ambatawa da suke kare mutum daga yin kaffara. To amma idan mutum ya rantse ce ba zai aikata abu kaza ba sai ya aikata da mantuwa ya hukuncin shi? Idan har akan mantuwa ya aikata babu wani abu a kan shi domin Allah baya k**a wanda ya aikata hakan da mantuwa sai dai idan da ganganci ne domin muna yin addu'a lokacin karanta amar-Rasulu muna cewa"Ya Allah Ubangijimmu ! kada ka k**a mu da abinda mukai da mantuwa ko mukai kuskure" Suratul-Bakara, aya ta karshe, kuma ya tabbata a hadisi ruwayar Muslim cewa Allah ya ce "Hakika na aikata"(ma'ana ya karba mana addu'ar). Saboda haka dukkan mutumin da ya yi rantsuwa akan ba zai yi abu kaza ba sai kuma ya aikata da mantuwa to babu wata kaffara akan shi, har ma da mutumin da ya rantse ba zai yi kaza ba ko kuma ya rantse sai ya yi kaza, sai aka tilasta shi da karfin tsiya to shima babu komai akan shi misali ya rantse ba zai shiga gidan wane ba sai aka sami samari majiya karfi s**a dauke shi cancakat s**a sa shi cikin gidan ko kuma ya rantse ba zai fita ba aka sa samarin s**a fitar da shi da karfin bala'I ko kuma s**a zane shi ko ma s**a ce za su kasha shi, shi ma babu wata kaffara akan shi, dalili kuwa shi ne fadar Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi "An yafe wa al'ummata Kuskure da Mantuwa da Dukkan abinda aka tilasta su akai" (dud da cewa malaman hadisi suna maganganu kan wannan hadisin) sai dai akwai ayar suratun-Nahli aya ta 106 fadin Allah mai girma da daukaka "Dukkan wanda ya kafirce ma Allah bayan ya yi imani (da Allah din) sai dai kawai wanda aka tilasta shi…" shi ne malamai suke cewa atilasta mutum ya kafirce wa Allah amma Allah ya ce bai kafurta ba b***e a tilastawa mutum ya warwre rantsuwar shi?.
Me ke sa mutum ya fita daga Rantsuwar shi? Abubuwan da suke san ya mutum ya fita daga rantsuwar da ya yi dayan abubuwa uku ne. abu na farko: ya aikata abinda ya rantse zai aikata, ko ya ki aikata abinda ya rantse ba zai aikata ba. abu na biyu: yin dogaciya wato ya fadi In sha Allahu a lokacin da ya yi rantsuwar k**ar yadda bayanai s**a gabata. Abu na uku kaffara, bayanai na nan na zuwa kan kaffara in Allah ya yarda. Wadan nan abubuwa uku su suke sa mutum ya fita daga rantsuwar da ya yi. Yanzu zamu kawo wadansu misalai na rantsuwa da s**an yawaitu a bakunan mutane muji hukuncin su.
Idan Mutum ya ce in har na auri wance ta saku. Idan mutum ya yi irin wannan maganar sai kuma Allah cikin ikon shi ya kaddari auren to ya sani fa bata sakuba domin Ma'aikin Allah ya ce "Babu alwashi ga Dan-adam cikin abinda ba ya mallaka, kuma babu 'yantawa cikin abinda baya mallaka, kuma babu saki ga Dan-adam cikin dukkanin abinda baya mallaka" Tirmizi ya ruwaito ya kuma ce hadisi ne kyakkyawa.
Idan mutum ya Rantse ba zai sayar ba ko ba zai aurar ba . ida mutum ya yi irin wannan rantsuwar sai kuma ya zo ya aurar ko ya zo ya sayar to zai yi kaffara sai dai idan mijin da aka aurarwa ya ki karba(ma'ana ya ce bai aura ba) ko wanda aka sayarwa ya ce bai saya ba to anan ba wata kaffara akan shi, zamu da kata akan wadannan misalai guda biyu har idan akwai tambaya sai a tuntuba k**ar yadda aka saba. Yan zu zamu shiga Magana akan:

Mai ake nufi da Kaffara.

Zamu ci gaba insha Allah



*Karatu Daga Zauren*
👇
```Ana muslim.```

➖➖➖➖➖➖➖➖

👉🏻✍🏻 ```• Duk mai Sha'awan Shiga Zauren ANA MUSLIM{☝أنا مسلم}
ta kafaar whatsApp sai ya/ta turo mana da suna, Adreshi, ta wannan Numbers namu```

*+2348066-686177*
_or_
*+234 802 909 9260*

Kuma za'a iya biyayanmu ta kafar facebook

https://www.facebook.com/zaurenanamuslim/

```Dokan da za'a kiyaye kafin Turo mana Suna```⚖🔨

*A TABBABTA ANYI CI KAKKEN SALLAMA KAFIN A TURO DA SUNA SLM KO ASLM BAZAI KARBU BA. SAI A KIYAYE*

Community

15/02/2019

🌂Wutar jahannama bata cin mai karanta wanan
addu'a
"Allahumma Ajirni Minan Naar"
Sau 7 bayan sallah Asuba da ta Maghrib.
In ka samu dama ka aika ma wani sai ta zama
sadaqatul-jariya gare ka kuma gare ni. Please

Picture of the year 2018 by foresight president
01/12/2018

Picture of the year 2018 by foresight president

Address

Northeast Of Nigeria
Northeast

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Apc Gombe & Bauchi State Forum posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Share on Facebook Share on Twitter Share on LinkedIn
Share on Pinterest Share on Reddit Share via Email
Share on WhatsApp Share on Instagram Share on Telegram