Khalifa bin Umar Hospital And Maternity Rigachiku.

Khalifa bin Umar Hospital And Maternity Rigachiku. is a hospital which offer 24 hours services khalifa bn umar community hospital is a hospital which offer medical services

25/12/2021

Jerin abinci da yake karawa mata masu shayarwa ruwan nono:

Abinda ya fi muhimmanci wajen samar da nono mai yawa da inganci ga mace mai shayarwa ita ce irin abincin da macen ke ci.

Yana da muhimmanci mace mai shayarwa ta rika shan ruwa mai tsafta da abinci mai ruwa-ruwa kamar Shayi da madara, kunu da sauransu.

Ga dai jerin abincin kamar haka:

1- Hatsi

Hatsi yana samar da ruwan nono ga mace Mai shayarwa sabida tana samarwa mata sinadaran bitamin E, B6 da B5 manganese, selenium da sauran su. Baya ga haɓaka samar da ruwan nono, yana intanta lafiyar garkuwar jikin yaro.

2- Alkama

Alkama wadda a turance ake kira Oatmeal tana da sinadarai masu gina jiki kuma ga saukin sarrafawa. Mai jego tana iya sarrafa alkama da madara ko da gyada domin kara dandano. Yana samar da ruwan nono sosai.

3- Alayyafo

Alayyafo yana daga cikin manyan manyan abinci dake karawa uwa ruwan nono. Hakanan suna da wadata a cikin abubuwan antioxidant, wanda ke taimakawa tsawan lokacin shayarwa.

4- Shinkafa ta gida

Yana da kyau mai jego ta dena amfani da shinkafar da aka sarrafa ta a kasashen waje wanda muka fi sani da shinkafar gwamnati ta koma amfani da tamu shinkafar ta gida saboda ita ke dauke da sinadirai da take taimakawa wajen inganta ruwan nono.

5- Karas

Idan mai jego na fama da karancin ruwan nono sai ta dage wajen cin karas ko kuma saka shi cikin abinci ko miyar. Karas na dauke da sinadarin vitaman A da wasu sinadaren da ke taimakawa wajen kara yawa da ingancin ruwan nono.

6- Tafarnuwa

Baya ga yana dauke da sinadarai masu amfani diyawa. A gefe guda, yana ƙara samar da nono da ma yana kare jariri daga abin mamakin ciki. Mace za ta iya ci haka ko anika shi a cikin abinci.

7- Dankalin Hausa

Dankalin hausa yana dauke da sinadarin potassium da kuma carbohydrate da ke matukar taimakawa wajen kara inganci ruwan nono da kuma magance kasala. Ana iya dafa dankalin a ci da miya ko a sarrafa ta wata hanyar.

8- Nonon Tsaniya

Madarar shanu da daya daga cikin abincin da ke kara yawa da inganci nono ga mai jego. Baya na nonon sauran ababen da ake fitarwa daga nonon kamar kindirmo da man shanu ko Yoghurt duk suna taimakawa suma.

9- Kunu

Kunu yana daya daga cikin abincin iyaye da kakanni ka bawa mai jego ta sha da zarar ta fara shayar da jaririn da ta haifa musamman a kasar Hausa. Ana iya sarrafa shi da gero ko masara a bawa mai.

Lafiya Uwar Jiki

22/12/2021
20/12/2021

Amfanin Kankana ga lafiyar jiki da ta Iyali:

1. Kankana na dauke da sinadarin “Lycopene” wanda yake kauda kwayoyin cutar daji

2. Kankana na samar da kariya daga ilollin zafin rana da kuma haske

3. Masu yawan shan kankana tana ingata lafiyar su domin da wuya su kamu da cutar Asthma saboda kankana na dauke da sinadarin “Vitamin C”

4. Kankana na samar da kariya ga cututtukan da s**a shafi zuciya

5. Ya’yan kankana nada mai, wannan man na taimakawa domin gina jiki da ingantashi

6. Ya’yan kankana na dauke da sinadarin “amino acids” wannan sinadarin na karawa Dan-adam lafiyar jiki da karfi da kuzarin jima’i

7. Ya’yan kankana na kara kaifin tunani

8. Idan mutum yayi rashin lafiya yana bukatan kankana domin kuzarin sa ya dawo

8. Kankana tana dauke da sinadarin dake bada kariya da rage cutar hawan jini

9. Uwargida zaki iya yin juice dinta domin inganta lafiyar ki da kara miki ni’ima ingantacciya dana mai gida kai har ma da yara tana gyara su.

Lafiya Uwar Jiki

18/12/2021

TYPHOID
---------------

Typhoid : typhoid ko enteric fever wata nau'in kwayoyin cuta ne (BAKTERIYA) da ake kiransu SALMONELLA TYPHY kuma ana kiransa SALMONELLA ENTERICA suke haifar da shi .

Mutum yana daukar wannan kwayar bakteriyan ne ta hanyar ruwan sha da kuma abinci .

Idan ruwan sha ko abinci ya gurbanta da bayan gida ko fitsarin mai ciwon, wanda hakan yana faruwa ne ta hanyoyi da yawa, to ta haka kwayar bakteriyar Typhoid take yaduwa .

SUNA DAGA CIKIN ALAMOMIN TYPHOID :

1- Zazzabi
2- mutuwar jiki
3- ciwon ciki
4- kumburin ciki
5- ciwon kai .

ME YASA TO SHI TYPHOID BA'A WARKEWA ?

Ba Ba'a warkewa bane , ana warkewa daga typhoid amma abinda yake faruwa shine :

1- Rashin shan magani yadda yakamata , yau anwayi gari shan magani barkatai yazama ruwa dare a najeriya , mafi yawa kwayoyin cutar ansaba musu da wannan maganin har yazama suna jurewa .

2- Za kaga mutum ana bashi maganin sati daya a ranan da yafara shan maganin idan yaji sauka shikenan ya rabu da maganin , Alhalin kwayar cutar Labewa tayi ba mutuwa .

3- Misali ace kwayar cutar ana samunshi daga gurbaceccen ruwa , To ana shan magani kuma ana cigaba da shan wannan ruwan kaga babu maganar warkewa .

HANYOYIN KARIYA DA CUTAN TYPHOID :

1- Duk matar da ba'a yarda da tsaftar ta ba a kauracewa abincin ta .

2- A kiyaye tsabtar muhalli da ta bayan gida dan kada kuda su samu wurin zama .

3- A rufe duk wani abinci da abin sha da aka ci , don kada kuda ta hau.

4- Kada aci kayan Lambu Irin su salat wanda ba dafasu akeyi ba ,sai an wanke da ruwan manda .

5- A guji bayan gida barkatai a hanya da gefen magudanan ruwa kovrijiya ko kogi.

6- A tabbatar an tace sannan a tafasa ruwan da aka debo daga rafi ko rijiya kafin a sha .

7- A tabbata an wanke hannaye da sabulu bayan anyi bayan gida ko kuma anyiwa yara tsarki kafin cin abinci .

GARGADI
A daina shan magani barkatai , kamar yadda mutane s**a saba , daga jin zazzabi ko ciwon kai sai s**e malaria da typhoid ne yake damunsu sai kaga suna ta shan maganin malaria da typhoid , batareda anyi bincike me yakawo zazzabin ba .

Lafiya Uwar Jiki

07/12/2021

MEYASA MATA KE GANIN FARIN RUWA YANA FITO MUSU KAFIN KO BAYAN GANIN PERIOD
DIN SU?

AKWAI MATSALA NE TATTARE DA HAKAN?

✓Normally mafi yawan mata suna samun fitowar farin ruwa a gabansu throughout menstrual circle dinsu.

✓Akalla mata dayawa suna ganin farin ruwa mai kauri ko salala, mara launi yana fito musu a kowace rana, adadin daya kai kimanin cikin shokalin shayi. Launin ruwan yana iya sauyawa daga farin madara, zuwa farin ruwa, ko kuma baki baki (brown).

✓Banbancin launin ruwan ko kaurin sa yana ta allaqa ne da hormonal changes na jikin ta a lokacin da yake fitowa.

✓Wannan fitan farin ruwa da mace take gani ta gaban ta kafin period dinta normal ne, babu matsala tattare da hakan. Process ne da ake kira "Leukorrhea" Wani lokacin yana iya kasance wa yellowish.

✓Hakan yana faruwa ne sbd yawan hormones "progesterone" dayake taruwa ajikin ta. A wannan gaban ana kiran yanayin da "luteal phase"

✓Wa'ennan hormones kamar su"progesterone" "oestrogen" "androgen" etc sauyin yanayin sune ajikin ta shike sawa tayi ta ganin "va**nal discharge" yana fito mata.

✓ Idan "estrogen" ne s**ayi yawa ajikin ta a lokacin, se ruwan ya kasance fari fari, mai yauki
kuma ruwa ruwa.

✓ Idan kuma "progesterone" ne s**ayi yawa ajikin ta, se ruwan ya kasance farin madara kuma mai kauri kauri.

✓Koma ya launin ruwan ya kasance, fari ne, ruwa ruwa ne, madara madara ne, yana da kauri ko akasin haka, muddin baya wari ko qarni, gaban mace baya zafi, kaikayi ko radadi, to wannan normal ne.

✓Aikin sa (ruwan) shine yayi flushing duk wani dattin va**na, wasu harmful germs, etc da kuma ya sa va**na ta zama moist all the time. Hakan yana nuna alamar the va**na and the
reproductive system is healthy and functional.

• WASU LOKUTA NE ZAKI TSAMMANCI GANIN FARIN RUWA A GABANKI; IDAN KINGANI BA DAMUWA BANE.

✓Normally mata suna iya samun bushewar gaba kamar na kwana 3 zuwa 4 kowane bayan yankewar period dinsu. bayan wannan kwanakin, farin ruwa mai danqo yakan sake bullowa wanda zayyi kamar kwana 4 zuwa 5 Kafin ovulation, alama she ta eggs sun fara developing. ana kiran shi da "follicular phase" that means a lokacin ne "eggs" (for ovulation) suke kokarin girma.

✓Idan kuma lokacin ovulation yayi, ruwan se ya
canza daga mai danqo zuwa fari mai yauki kuma mara kauri (salala) haka. A wannan lokacin yana kara yawa sosai fiye da na kullum a da. Shi kuma ana kiran shi "egg white".
Aikin sa shine ya taimaka wajen santsin s***m a va**na da cervix domin ya samu daman isowa kwai da yake jiransa for ovulation.

✓Sannan Mata dayawa suna amfani da ganin wannan ruwan a matsayin alama ta ovulation dinsu, hakan yana taimaka musu wajen samun ciki da wuri ko kuma kaura cewa yin cikin. Wannan process din shi ake kira da "natural family planning" ko "fertility awareness method".

1. ✓Idan ruwa ruwan ya kasance mara kauri (salala) to ana kyautata zaton shine "fertile" (i.e ciki zai iya shiga kenan in Kwan ya samu s***m). Sbd a lokacin kwan zai sauka zaman jira.

2. ✓ Idan kuma ruwa ruwan ya kasance fari mai kauri to shi kuma shine "infertile" (wanda ko an sadu ciki bazai shiga ba) sbd kwan har ya riqa, karfin sa ya kare, yanzu sedai ya harziqa, se facewa.

✓To irin wannan ruwa ruwan mai kauri zaki cigaba da gani daga bayan ovulation har zuwa wani period din.

✓Daga bayan ovulation din zuwa wani period din, yawan fitowar ruwan zai na raguwa a hankali, yana zamowa mai kauri kuma mai danqo again, wani lokaci har zaki iya jinsa kamar wata gum ko glue.

✓On average dai, yana kaiwa irin kwana 11 zuwa 14. That is tsakanin ovulation dinki zuwa wani period dinki kenan.

✓Wasu lokuta kina iya ganinsa yellowish haka kafin period dinkin.

✓Idan mace taga wani irin brown discharge a bayan period dinta kuma, bayan jinin ya dauke, se ta sake ganin wani baki baki haka brown ya zo mata, to shi din yana kasance wa tsohuwar jini ne daya daskare bai samu daman fitowa ba last time. Shine yanzu yake kamo hanya.

✓Idan kuma brown discharge din kafin period ne fa? Ko kuma taga jinin Dan digo digo haka a lokacin da take tsammanin period dinta, to shi
kuma yana iya kasance wa sign ne na "implantation" daga farko farkon pregnancy. Maza se kiyi kokari kije pregnancy test domin a tabbatar da hakan ko akasin hakan. (In kin samu congratulations )

• ME KE JAWO KO SANADIN FITOWAR FARIN RUWAN?

Akwai kamar category guda biyu:
1. Akwai wanda yake normal; sbd hormonal
changes.
2. Akwai kuma wanda yake abnormal: sbd infection.

1. NORMAL:
(A1).✓ yana iya kasance wa alama she ta reproductive system na mace yana functioning properly. Sbd kasance war discharge din mara kauri ne, mai yauki ne kuma mai santsi. Sannan baya wari ko qarni. Wasu suna kiran shi da "egg white mucus"

(B1). ✓Normal side effects na family planning; sakamon sauyin yanayin levels na hormones da yake jawowa, hakan yana sawa normal va**nal discharge ya karu shima.

(C1). ✓Pregnancy: wani lokaci yawan va**nal discharge kafin lokacin normal period dinki yazo yana iya zama sign ne na daukan ciki. Musamman ma idan mucus din ya kasance mai kauri kuma ruwan madara madara.

2. ABNORMAL:
(A2). ✓STIs(Sexually Transmitted Infections): kamar su Gonorhea, chylamydia, Trichomonas duk suna jawo mace tayi ta ganin fitan ruwa ta gaban ta. Gonorhea da chylamydia su yawanci basa ma nuna symptoms, sannan discharge dinsu yana nan ne yellowish haka kamar diwa diwa.

✓Shi kuma Trichomonas; discharge din da yake jawowa yana yellow ko Kore ne haka, sannan yana nuna symptoms dinsa kamar qarnin kifi kifi, kuma ga kaikayin tsiya.

(B2). ✓Candidiasis (yeast infection): shi kuma discharge dinsa fari ne mai kauri, kamar farin madara. Yawanci yafi faruwa a lokaci kafin mace taga period dinta. Yana da symptoms kamar kaikayi da jin zafi zafi a gaban mace (ta ciki da ta wajen).

(C2). ✓Bacterial Vaginosis: shima wata infection dinne da yake jawo discharge mai K**a da toka toka(gray-white) sannan yana sa warin gaba kamar qarnin kifi kifi haka.

✓ K**ar yadda kuka gani a sama tin farko, ainihin ababen da ke sa fitowar farin ruwa kenan. Da kuma yawancin lokuta da ruwa yake fito ma mata.

SHAWARA
✓Duk sanda kika ga ruwa yana fitowa ta gaban ki, kana fari ne, milk milk ne, mai kauri ne ko salala ne, mai yauki ne ko mai santsi ne, muddin baya wari kuma baya sa kaikayi ko radadi ko jin zafin gaba ko kuma yayin fitsari ko saduwa da miji, kawai ahlun salun yake fitowa abinsa, to karki tada hankali wannan normal ne. Alama she na jikin ki a matsayin ki mace, yana aiki yadda yakamata kuma cikin kocin lfyy.

✓Idan kuma kinga ruwa yana fito miki koma ya launin sa yake, kuma se tare da hakan akwai zafin gaba, kaikayin gaba, ko warin gaba, kumburin gaba, kurajen gaba ko dadewar fatar shi, ta ciki ko ta wajensa, ko kuma duka biyun, to maza maza kiyi saurin zuwa asibiti domin magani.

Allah Yabamu Lafiya Gabaki Dayanmu.

17/08/2021

YADDA ZUCIYA KE BUGAWA

Allah Gwani | Ko ka san sau nawa zuciyarka ke harbawa kowace rana?

Zuciya ita ce famfon da ke harbawa domin buga jini zuwa dukan sassan jiki ba-dare-ba-rana domin ci gaban rayuwa. Rayuwa na tsayawa da tsayawar aikin zuciya.

Kwatankwacin girman zuciyar mutum ya kai girman dunƙulallen hannun mutum. Kuma zuciya tana bugawa sau 60 — 100 duk minti ɗaya yayin hutu, wato yayin da ba aiki ko motsa jiki ake yi ba. Saboda adadin harbawar zuciya [cikin minti ɗaya] na ƙaruwa yayin atisaye ko motsa jiki.

A kowace rana kuwa, zuciya na harbawa kimanin sau dubu ɗari (100,000). Inda take buga jini da ya kai yawan galan dubu biyu a kowace rana. Har wa yau, zuciyar na buga jini zuwa jijiyoyin jinin da tsayinsu ya kai mil dubu sittin (60,000 miles) in da za a warware tsayinsu.

Zuciya, sannu da aiki!

Kuyi SUBSCRIBE a YOUTUBE-CHANEL kuma ka danna alamar kararrawa, domin ganin VEDEO yadda zuciya ke bugawa da zaran mun ɗaura ta wannan Link
👇👇👇👇👇👇👇�
https://www.youtube.com/channel/UCmC9fMpvNGwheErpsSvVZyA

Address

Rigachikun

Telephone

+2348100613544

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Khalifa bin Umar Hospital And Maternity Rigachiku. posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Practice

Send a message to Khalifa bin Umar Hospital And Maternity Rigachiku.:

Share

Share on Facebook Share on Twitter Share on LinkedIn
Share on Pinterest Share on Reddit Share via Email
Share on WhatsApp Share on Instagram Share on Telegram

Category