Arrida Chemist Shinkafi

Arrida Chemist Shinkafi To encourage people to adopt and sustain health promoting life style and practices

๐™”๐˜ผ๐™‰๐™•๐™ ๐™ˆ๐™๐™‰๐˜ผ ๐™‡๐™Š๐™†๐˜ผ๐˜พ๐™„๐™‰ ๐™•๐˜ผ๐™•๐™•๐˜ผ๐˜ฝ๐™„๐™‰ ๐˜พ๐™„๐™•๐™Š๐™‰ ๐™Ž๐˜ผ๐™๐™๐™Š, ๐™ˆ๐˜ผ๐™‡๐˜ผ๐™๐™„๐˜ผ ๐™๐˜ผ ๐™”๐˜ผ๐™’๐˜ผ๐™„๐™๐˜ผ ๐˜ผ ๐™‚๐˜ผ๐™๐™„Daga: Arrida Chemist๐Ÿ’Š ShinkafiMun sha bayar da shawarw...
29/07/2024

๐™”๐˜ผ๐™‰๐™•๐™ ๐™ˆ๐™๐™‰๐˜ผ ๐™‡๐™Š๐™†๐˜ผ๐˜พ๐™„๐™‰ ๐™•๐˜ผ๐™•๐™•๐˜ผ๐˜ฝ๐™„๐™‰ ๐˜พ๐™„๐™•๐™Š๐™‰ ๐™Ž๐˜ผ๐™๐™๐™Š, ๐™ˆ๐˜ผ๐™‡๐˜ผ๐™๐™„๐˜ผ ๐™๐˜ผ ๐™”๐˜ผ๐™’๐˜ผ๐™„๐™๐˜ผ ๐˜ผ ๐™‚๐˜ผ๐™๐™„

Daga: Arrida Chemist๐Ÿ’Š Shinkafi

Mun sha bayar da shawarwari a baya, yanzu ma zamu sake mai-maitawa.

Ga kaษ—an daga shawarwarin

Wanda basu kamu da malaria ba su bi Wannan hanyoyin domin samun kariya

1. Kwana cikin gidan sauro (insecticide treated net )
2. Gyara magudanar ruwa. Yanke ciyawu a cikin unguwa
3. Sanya net mai inganci a window ko kofa
4. A daina barin ruwan datti ya taru ba tare da an kwashe ba ko an share

Idan an kamu da malaria kuma

1. Ayi saurin ganin Likita saboda ayi gwaji a tabbatar malaria din ce
2. A siya magunguna daga kemis ko Pharmacy wanda aka yadda da ingancin maganinsu
3. A shanye magungunan k**ar yadda likitoci s**a bada umurni a yi
4. Wadanda likita ya dubasu, kuma har sun shanye magani ko an musu allurai amma ciwon baiyi sauki ba ko kuma yana kara tsananta, ayi gaggawar komawa wurin likita.

Idan ba a magance malaria ba yakan kawo matsaloli sosai, harda rasa rai

Fatan sakon ya isa ga kowa.

Allah Ya kare mu da iyalan mu. Amin

๐˜ผ๐˜ฝ๐™๐™‰๐˜ฟ๐˜ผ ๐™”๐˜ผ๐™†๐˜ผ๐™ˆ๐˜ผ๐™๐˜ผ ๐˜ผ๐™”๐™„ ๐™‡๐™Š๐™†๐˜ผ๐˜พ๐™„๐™‰ ๐™ƒ๐˜ผ๐™„๐™ƒ๐™๐™’๐˜ผ ๐˜ผ ๐™‡๐™„๐™†๐™„๐™๐˜ผ๐™‰๐˜พ๐™€Daga: Arrida Chemist ๐Ÿ’Š ShinkafiA lissafin masana kiwon lafiya ana kyautat...
07/06/2024

๐˜ผ๐˜ฝ๐™๐™‰๐˜ฟ๐˜ผ ๐™”๐˜ผ๐™†๐˜ผ๐™ˆ๐˜ผ๐™๐˜ผ ๐˜ผ๐™”๐™„ ๐™‡๐™Š๐™†๐˜ผ๐˜พ๐™„๐™‰ ๐™ƒ๐˜ผ๐™„๐™ƒ๐™๐™’๐˜ผ ๐˜ผ ๐™‡๐™„๐™†๐™„๐™๐˜ผ๐™‰๐˜พ๐™€

Daga: Arrida Chemist ๐Ÿ’Š Shinkafi

A lissafin masana kiwon lafiya ana kyautata zaton mace mai ciki za ta haihu ne tsakanin makonni 38 zuwa 42.

Da zaran mace tashiga makonnin nan zatafara jin wadannan alamomin

(alamomin nakuda)
- Yawan fitsari
- Daurewar mara
- Ciwon mara
- Ciwon baya
- Nauyin Ciki
- fitar da wani Abu mai k**ar majina a bakin mahaifa.

A duk lokocin da kika fara samun wadannan alamomi kije kiga likita kiyi magana da ingozuman ki akan naโ€™kuda da kuma hanyoyin da zakibi ki haihu lami lafiya, da kuma me yak**ata ki tanada kafin lokacin haihuwar tazo.

Sabida haihuwar gida ba tare da likita ba tanada hatsari sosai musamman ga wadannan mata :

1- Mace mai ciki na farko
2- Mace mai ciki na shidda zuwa gaba.
3- Idan kwanciyar yaro baiyi daidai ba.
4- Wacce take samun alamun kunburin kafa.
5- Idan ana tsammanin tagwaye ne.
6- Idan mace ta taba samun zubar jini bayan haihu.
7- Idan mace antaba yi mata tiyata na haihuwa.
8- Macen da batada tsawo (gajera)
9- Mace mai rashin jini.
10- Matar da take samun zubar jini.

Sabida haka muna kira ga dukkanin mata kada suyi gangacin haihuwa a gida kuma su kadai ba tare da likita ba domin tana da hatsari sosai.

IDAN AKA SAMU AKASI AKA HAIHU A GIDA KUMA KE KADAI:

Ko an samu akasi aka haifi yaro a gida da wata matsala dole za'a dauko yaro zuwa asibiti, amma kafin azo asibity abin da ya k**ata ayi sune:

1- Da zaran an haifi yaro adan jinkir ta kafin a yanke cibiya da sabuwar reza a kalla minti daya zuwa biyu.

2- Ayi kokorin share majinar dake bakin yaro da auduga mai tsafta.

Yin hakan gaskiya zai taaimaka wajen ceton rayuwar jarirai.

3- Lokocin da aka haifi yaro a kifar da shi a kirjin mamar sa ( skin to skin contact).

4- Kada ayiwa jariri wanka, a daukeshi a yadda yake zuwa asibiti.

5- A taimaka a sanya jariri a nono tun kafin aje asibity, da zaran a goge majinar bakin sa a tura shi ga nono.

6- Kada a sanya komai a cibiyar yaro da sunan magani sai anje asibity.

Allah ya saukar da masu juna biyu lafiya Amin

Barkammu da safiyar Juma'a.

โ˜ž๐Š๐€๐’๐‡๐„๐ƒ๐ˆ๐๐Š๐” ๐Œ๐€๐“๐€๐ ๐™๐€๐Œ๐€๐๐ˆ ๐Ÿ”ž๐ƒ๐š๐ ๐š: ๐‘จ๐’“๐’“๐’Š๐’…๐’‚ ๐‘ช๐’‰๐’†๐’Ž๐’Š๐’”๐’•๐Ÿ’Š๐‘บ๐’‰๐’Š๐’๐’Œ๐’‚๐’‡๐’Š๐‘ฉ๐ฎ๐ฅ๐ฅ๐จ๐ฐ๐š๐ซ ๐ฌ๐š๐›๐š๐›๐›๐ข๐ง ๐ฆ๐š๐ ๐š๐ง๐ข๐ง ๐๐š ๐š๐ค๐ž๐œ๐ž๐ฐ๐š ๐ฐ๐š๐ข ๐˜๐š๐ง๐š ๐๐š๐ฐ๐จ๐ฐ๐š ๐๐š ๐ฏ๐š๐ ๐ข๐ง๐ข๐ญ๐ฒ ...
14/03/2023

โ˜ž๐Š๐€๐’๐‡๐„๐ƒ๐ˆ๐๐Š๐” ๐Œ๐€๐“๐€๐ ๐™๐€๐Œ๐€๐๐ˆ ๐Ÿ”ž

๐ƒ๐š๐ ๐š: ๐‘จ๐’“๐’“๐’Š๐’…๐’‚ ๐‘ช๐’‰๐’†๐’Ž๐’Š๐’”๐’•๐Ÿ’Š๐‘บ๐’‰๐’Š๐’๐’Œ๐’‚๐’‡๐’Š

๐‘ฉ๐ฎ๐ฅ๐ฅ๐จ๐ฐ๐š๐ซ ๐ฌ๐š๐›๐š๐›๐›๐ข๐ง ๐ฆ๐š๐ ๐š๐ง๐ข๐ง ๐๐š ๐š๐ค๐ž๐œ๐ž๐ฐ๐š ๐ฐ๐š๐ข ๐˜๐š๐ง๐š ๐๐š๐ฐ๐จ๐ฐ๐š ๐๐š ๐ฏ๐š๐ ๐ข๐ง๐ข๐ญ๐ฒ ๐ฐ๐š๐ญ๐จ ๐Ÿ๐š๐ญ๐š๐ซ ( ๐›๐ฎ๐๐ฎ๐ซ๐œ๐ข ) ๐ฐ๐š๐ง๐ง๐š๐ง ๐›๐š ๐ ๐š๐ฌ๐ค๐ข๐ฒ๐š ๐›๐š๐ง๐ž ๐ค๐š๐ซ๐ฒ๐š๐œ๐ž ๐ฌ๐ž๐๐š๐ข ๐ฒ๐š ๐ก๐š๐๐๐š๐ฌ๐š ๐ฆ๐š๐ค๐ฎ ๐Ÿ‘‡

1.๐œ๐š๐ง๐œ๐ž๐ซ
2.๐ข๐ง๐Ÿ๐ž๐œ๐ญ๐ข๐จ๐ง
3.๐จ๐ฏ๐š๐ซ๐ข๐š๐ง ๐œ๐ฒ๐ฌ๐ญ
4.๐Ÿ๐š๐›๐ซ๐จ๐ข๐ ๐ฅ๐š๐ฒ๐ž๐ซ
5.๐ข๐ง๐Ÿ๐ž๐ซ๐ญ๐ข๐ฅ๐ข๐ญ๐ฒ ๐ก๐š๐ง๐š ๐ก๐š๐ข๐ก๐ฎ๐ฐ๐š
๐ž.๐ญ.๐œ

๐๐”๐ƒ๐”๐‘๐‚๐ˆ ๐๐€ ๐–๐”๐‚๐‚๐ˆ๐ ๐†๐€๐ƒ๐ˆ
(๐€๐ซ๐ญ๐ข๐Ÿ๐ข๐œ๐ข๐š๐ฅ ๐•๐ข๐ซ๐ ๐ข๐ง๐ข๐ญ๐ฒ ๐‡๐ฒ๐ฆ๐ž๐ง)

๐‡๐˜๐Œ๐„๐ :- ๐ฐ๐š๐ญ๐š ๐Ÿ๐š๐ญ๐š ๐œ๐ž ๐๐š ๐ญ๐š๐ค๐ž ๐ ๐š๐›๐š๐ง ๐ฆ๐š๐ญ๐š ๐๐š๐› ๐๐š ๐œ๐ž๐ซ๐ฏ๐ข๐ฑ, ๐š ๐ก๐š๐ฎ๐ฌ๐š๐ง๐œ๐ž ๐ญ๐š๐ง๐š ๐๐š๐ฎ๐ค๐š๐ง ๐ฌ๐ฎ๐ง๐š๐ง ๐๐”๐ƒ๐”๐‘๐‚๐ˆ, ๐ค๐ฎ๐ฆ๐š ๐ซ๐š๐ฌ๐ก๐ข๐ง๐ญ๐š ๐ฌ๐ก๐ข๐ง๐ž ๐ซ๐š๐ฌ๐ก๐ข๐ง ๐›๐ฎ๐๐ฎ๐ซ๐œ๐ข. ๐…๐š๐ญ๐š๐ซ ๐›๐š๐ญ๐š ๐๐š ๐ค๐š๐ซ๐Ÿ๐ข ๐ฌ๐จ๐ฌ๐š๐ข ๐ค๐ฎ๐ฆ๐š ๐ซ๐ฎ๐ฐ๐š ๐ฌ๐ฎ๐ค๐š๐ง ๐ข๐ฒ๐š ๐ฐ๐ฎ๐œ๐ž๐ฐ๐š ๐ญ๐š ๐œ๐ข๐ค๐ข๐ง๐ญ๐š, ๐ญ๐š๐ง๐š ๐๐š๐ฎ๐ค๐ž ๐ƒ๐š ๐ค๐š๐ง๐š๐ง๐š๐ง ๐ก๐š๐ง๐ฒ๐จ๐ฒ๐ข ๐ง๐š ๐ฃ๐ข๐ง๐ข, ๐ฌ๐ก๐ข๐ฒ๐š๐ฌ๐š ๐Ÿ๐š๐ฌ๐ก๐ž๐ฐ๐š ๐ค๐จ ๐ญ๐ฌ๐š๐ ๐ž๐ฐ๐š๐ซ๐ญ๐š ๐ฒ๐š๐ค๐š๐ง๐ฌ๐š ๐ฃ๐ข๐ง๐ข ๐ฒ๐š ๐Ÿ๐ข๐ญ๐จ.

๐Œ๐š๐Ÿ๐ข ๐š๐ค๐š๐ฌ๐š๐ซ๐ข ๐ฐ๐š๐ง๐ง๐š๐ง ๐Ÿ๐š๐ญ๐š ๐ญ๐š๐ค๐š๐ง ๐ญ๐ฌ๐š๐ ๐ž ๐ง๐ž ๐ข๐๐š๐ง ๐๐š๐ฒ๐š ๐๐š๐ ๐š ๐œ๐ข๐ค๐ข๐ง ๐ฐ๐š๐๐š๐ง๐ง๐š๐ง ๐š๐›๐ฎ๐›๐ฎ๐ฐ๐š ๐ฌ๐ฎ๐ค๐š ๐Ÿ๐š๐ซ๐ฎ ๐ ๐š ๐ฆ๐š๐œ๐œ๐ž:

1. ๐ˆ๐๐š๐ง ๐š๐ง ๐ฌ๐š๐๐ฎ ๐๐š ๐ฆ๐š๐œ๐ž (๐œ๐จ๐ฉ๐ฎ๐ฅ๐š๐ญ๐ข๐จ๐ง).
2. ๐–๐š๐ฃ๐ž๐ง ๐ง๐ž๐ฆ๐š๐ง ๐Ÿ๐ข๐ญ๐š๐ซ ๐๐š ๐ฌ๐ก๐š'๐š๐ฐ๐š ๐๐š ๐ฐ๐š๐ง๐ข ๐€๐›๐ฎ ๐ฆ๐š๐ข ๐ค๐š๐ซ๐Ÿ๐ข (๐ฏ๐š๐ ๐ข๐ง๐š๐ฅ๐ข๐ง๐ฌ๐ž๐ซ๐ญ๐ข๐จ๐ง ๐จ๐ซ ๐ฆ๐š๐ฌ๐ญ๐ฎ๐›๐š๐ญ๐ข๐จ๐ง). 3.๐˜๐š๐ฐ๐š๐ง ๐ญ๐ฌ๐š๐ฅ๐ฅ๐ž ๐ค๐จ ๐ฒ๐š๐ฐ๐š๐ง ๐ก๐š๐ฐ๐š๐ง ๐ฆ๐š๐ฌ๐ก๐ข๐ง, ๐ค๐ž๐ค๐ž, ๐๐จ๐ค๐ข ๐ค๐จ ๐ฃ๐š๐ค๐ข ๐ค๐จ ๐๐š๐ฎ๐ค๐š๐ซ ๐ค๐š๐ฒ๐š ๐ฆ๐š๐ข ๐ง๐š๐ฎ๐ฒ๐ข ๐š๐ฒ๐ข ๐ญ๐š๐Ÿ๐ข๐ฒ๐š.

๐Š๐š๐ฌ๐š๐ง๐œ๐ž๐ฐ๐š๐ซ ๐ฆ๐š๐Ÿ๐ข ๐ฒ๐š๐ฐ๐š๐ง ๐Œ๐š๐ณ๐š ๐ฌ๐ฎ๐ค๐š๐ง๐ฒ๐ข ๐š๐ฆ๐Ÿ๐š๐ง๐ข ๐๐š ๐Ÿ๐š๐ฌ๐ก๐ž๐ฐ๐š๐ซ ๐ฐ๐š๐ง๐ง๐š๐ง ๐Ÿ๐š๐ญ๐š ๐๐š ๐Ÿ๐ข๐ญ๐š๐ซ ๐ฃ๐ข๐ง๐ข ๐ฐ๐š๐ฃ๐ž๐ง ๐ ๐ฐ๐š๐๐š ๐›๐ฎ๐๐ฎ๐ซ๐œ๐ข๐ง '๐˜๐š ๐ฆ๐š๐œ๐ž ๐๐จ๐ง ๐ญ๐š๐›๐›๐š๐ญ๐š๐ซ๐ฐ๐š ๐›๐š๐ญ๐š ๐ญ๐š6๐š ๐ฌ๐š๐๐ฎ๐ฐ๐š ๐๐š ๐ค๐จ ๐ฐ๐š๐ง๐ž ๐ง๐š๐ฆ๐ข๐ฃ๐ข ๐›๐š.

๐’๐š๐ข ๐ญ๐ฎ๐ซ๐š๐ฐ๐š ๐ฌ๐ฎ๐ค๐š ๐ณ๐š๐ฎ๐ง๐š ๐ฌ๐ฎ๐ค๐š๐ฒ๐ข ๐ง๐š๐ณ๐š๐ซ๐ข๐ง ๐ฒ๐ข๐ง ๐‰๐š๐›๐ฎ๐ง ๐ฐ๐š๐ง๐ง๐š๐ง ๐…๐š๐ญ๐š๐ซ (๐ฆ๐š๐ข ๐ฌ๐ฎ๐ง๐š ๐€๐ซ๐ญ๐ข๐Ÿ๐ข๐œ๐ข๐š๐ฅ ๐•๐ข๐ซ๐ ๐ข๐ง๐ข๐ญ๐ฒ ๐‡๐ฒ๐ฆ๐ž๐ง) ๐๐จ๐ฆ๐ข๐ง ๐ฆ๐š๐ญ๐š๐ง ๐๐š ๐ฌ๐ฎ๐ค๐š ๐ซ๐š๐ฌ๐š ๐›๐ฎ๐๐ฎ๐ซ๐œ๐ข ๐ค๐š๐Ÿ๐ง
๐š๐ฎ๐ซ๐ž.

๐’๐ก๐ข ๐ฐ๐š๐ง๐ง๐š๐ง ๐…๐€๐Š๐„ ๐‡๐˜๐Œ๐„๐ ๐ซ๐จ๐›๐š ๐œ๐ž ๐๐š
๐š๐ค๐š๐ฒ๐ข๐ญ๐š ๐๐š ๐ฌ๐ข๐ง๐š๐๐š๐ซ๐ž ๐ฆ๐š๐ฌ๐ฎ ๐ง๐š๐ซ๐ค๐ž๐ฐ๐š ๐๐š๐ณ๐š๐ข ๐๐š๐œ๐ž ๐๐š ๐ฃ๐ข๐ค๐ข๐ง ๐ฆ๐ฎ๐ญ๐ฎ๐ฆ (๐ฉ๐ซ๐จ๐ฌ๐ญ๐ก๐ž๐ญ๐ข๐œ ๐ข๐ง ๐ง๐š๐ญ๐ฎ๐ซ๐ž) ๐ฒ๐š๐ง๐๐š ๐ข๐๐š๐ง ๐ฆ๐š๐œ๐ž๐ง ๐๐š ๐ญ๐š ๐ซ๐š๐ฌ๐š ๐›๐ฎ๐๐ฎ๐ซ๐œ๐ข๐ง๐ญ๐š ๐ญ๐š๐ฌ๐š ๐ณ๐š๐ข ๐ณ๐š๐ฎ๐ง๐š ๐๐š๐ข๐๐š๐ข ๐ ๐ฎ๐ซ๐›๐ข๐ง ๐ญ๐š, ๐ฌ๐š๐ง๐ง๐š๐ง ๐๐š ๐ณ๐š๐ซ๐š๐ซ ๐ญ๐š ๐ฌ๐š๐๐ฎ ๐๐š ๐š๐ง๐ ๐จ๐ง๐ญ๐š ๐ฐ๐š๐ง๐ข ๐ฃ๐š๐ง ๐ฌ๐ข๐ง๐š๐๐š๐ซ๐ข ๐ณ๐š๐ข ๐Ÿ๐š๐ฌ๐ก๐ž ๐๐š๐ ๐š ๐œ๐ข๐ค๐ข๐ง
๐€๐ซ๐ญ๐ข๐Ÿ๐ข๐œ๐ข๐š๐ฅ ๐•๐ข๐ซ๐ ๐ข๐ง๐ข๐ญ๐ฒ ๐‡๐ฒ๐ฆ๐ž๐ง ๐๐ข๐ง ๐ฆ๐š๐ข ๐ค๐š๐ฆ๐š ๐๐š ๐ฃ๐ข๐ง๐ข, ๐ญ๐จ๐ก, ๐๐š๐ณ๐š๐ซ๐š๐ซ ๐š๐ง๐ ๐จ ๐ฒ๐š๐ ๐š ๐ก๐š๐ค๐š ๐ฌ๐š๐ข ๐ฒ๐š ๐ณ๐š๐œ๐ข ๐ฆ๐š๐ญ๐š๐ซ ๐ฌ๐š ๐›๐ฎ๐๐ฎ๐ซ๐ฐ๐š ๐ฒ๐š ๐š๐ฎ๐ซ๐ž๐ญ๐š.

๐๐š๐›๐ฎ ๐ฌ๐ก๐š๐ค๐ค๐š๐ก ๐š๐ค๐ฐ๐š๐ข ๐š๐›๐ฎ๐›๐ฎ๐ฐ๐š๐ง ๐๐š ๐ฒ๐š ๐ค๐š๐ฆ๐š๐ญ๐š ๐ฆ๐š๐ญ๐š ๐ฌ๐ฎ ๐ค๐ฎ๐ฅ๐š ๐๐š ๐ฌ๐ฎ ๐ ๐š๐ฆ๐ž ๐๐š:(๐ฐ๐š๐ง๐š๐ง ๐…๐š๐ค๐ž ๐‡๐ฒ๐ฆ๐ž๐ง) ๐๐ข๐ง.

๐Š๐š๐ฌ๐š๐ง๐œ๐ž๐ฐ๐š๐ซ ๐›๐š๐ฒ๐š๐ง ๐ฌ๐š๐๐ฎ๐ฐ๐š (๐Ÿ๐š๐ค๐ž ๐ก๐ฒ๐ฆ๐ž๐ง ) ๐ณ๐š๐ข ๐ข๐ฒ๐š
๐Ÿ๐ข๐ญ๐จ๐ฐ๐š, ๐ข๐ง ๐ค๐ฎ๐ฆ๐š ๐›๐š๐ข ๐Ÿ๐ข๐ญ๐จ ๐›๐š ๐ณ๐š๐ข ๐ข๐ฒ๐š ๐ง๐š๐ซ๐ค๐ž๐ฐ๐š ๐š๐œ๐ข๐ค๐ข๐ง ๐ ๐š๐›๐š๐ง ๐ฆ๐š๐œ๐ž, ๐๐จ๐ง ๐ก๐š๐ค๐š ๐ณ๐š๐ข ๐ข๐ฒ๐š ๐ค๐š๐ฐ๐จ ๐ฆ๐š๐ญ๐ฌ๐š๐ฅ๐จ๐ฅ๐ข๐ง ๐ฅ๐š๐Ÿ๐ข๐ฒ๐š ๐ ๐š ๐ฆ๐š๐œ๐ž๐ง ๐๐š๐ญ๐š๐ฒ๐ข ๐š๐ฆ๐Ÿ๐š๐ง๐ข ๐๐š๐ฌ๐ก๐ข.

๐‡๐š๐ค๐š ๐ณ๐š๐ฅ๐ข๐ค๐š ๐ฃ๐š๐ง ๐ซ๐ฎ๐ฐ๐š๐ง ๐๐š ๐ฐ๐š๐ง๐ง๐š๐ง ๐…๐€๐Š๐„ ๐‡๐˜๐Œ๐„๐ ๐๐ข๐ง ๐ค๐ž ๐Ÿ๐ข๐ญ๐š๐ซ๐ฐ๐š ๐ฆ๐š๐ข ๐ค๐š๐ฆ๐š ๐๐š ๐ฃ๐ข๐ง๐ข, ๐ฌ๐ก๐ข๐ฆ๐š
๐ณ๐š๐ข ๐ข๐ฒ๐š ๐œ๐š๐ง๐ณ๐š ๐ค๐š'๐ข๐๐š๐ซ ๐ญ๐ฌ๐š๐Ÿ๐ญ๐š๐ซ ๐ฏ๐š๐ ๐ข๐ง๐š ๐ฆ๐š๐œ๐ž, ๐ฌ๐š๐›๐จ๐๐š ๐œ๐ข๐ค๐ข๐ง๐ฌ๐š ๐š๐ค๐ฐ๐š๐ข (๐œ๐ก๐ž๐ฆ๐ข๐œ๐š๐ฅ๐ฌ) ๐๐š๐ฎ๐ค๐ž ๐๐š ๐ค๐š๐ฅ๐š๐ซ ๐‰๐€, ๐๐จ๐ง ๐ก๐š๐ค๐š ๐ฐ๐š๐ง๐ง๐š๐ง ๐š๐›๐ฎ๐ง ๐ณ๐š๐ข ๐ข๐ฒ๐š ๐ค๐š๐ฐ๐จ ๐ฆ๐š๐ญ๐ฌ๐š๐ฅ๐จ๐ฅ๐ข ๐ค๐š๐ฆ๐š๐ซ ๐ก๐š๐ค๐š:

1*๐˜๐š๐ง๐š ๐œ๐š๐ง๐ณ๐š ๐ฒ๐š๐ง๐š๐ฒ๐ข๐ง ๐ฌ๐ข๐ง๐š๐๐š๐ซ๐š๐ง ๐๐š๐ค๐ž
๐ค๐ข๐ฒ๐š๐ฒ๐ž ๐ฏ๐š๐ ๐ข๐ง๐š.
2.๐˜๐š๐ง๐š ๐ข๐ฒ๐š ๐ค๐š๐ฐ๐จ ๐œ๐š๐ง๐œ๐ž๐ซ ๐จ๐Ÿ ๐ฏ๐š๐ ๐ข๐ง๐š.
3*๐˜๐š๐ง๐š ๐ญ๐จ๐ฌ๐ก๐ž ๐ฆ๐š๐ก๐š๐ข๐Ÿ๐š ๐š๐ค๐š๐ฌ๐š ๐ฌ๐š๐ฆ๐ฎ๐ง
๐ก๐š๐ข๐ก๐ฎ๐ฐ๐š.
4*๐˜๐š๐ง๐š ๐œ๐š๐ง๐ณ๐š ๐ญ๐ฌ๐š๐ซ๐ข๐ง ๐ก๐š๐ข๐ฅ๐š๐ซ ๐ฆ๐š๐œ๐ž (๐ญ๐š
๐ฒ๐š๐ง๐๐š ๐ก๐š๐ข๐ฅ๐š๐ซ ๐ณ๐š๐ญ๐š ๐ซ๐ข๐ค๐ข๐œ๐ž).
5*๐˜๐š๐ง๐š ๐ค๐š๐ฐ๐จ ๐ซ๐š๐ฌ๐ก๐ข๐ง ๐ก๐š๐ข๐ก๐ฎ๐ฐ๐š (๐ข๐ง๐Ÿ๐ž๐ซ๐ญ๐ข๐ฅ๐ข๐ญ๐ฒ)
๐ ๐š ๐ฆ๐š๐ณ๐š.

๐‰๐š๐ง ๐ก๐š๐ง๐ค๐š๐ฅ๐ข ๐ ๐š ๐ฆ๐š๐ณ๐š ๐š๐ง๐ ๐š๐ฒ๐ž, ๐๐š ๐ฌ๐š๐ข ๐ฆ๐š๐œ๐œ๐ž ๐ญ๐š ๐ฌ๐š๐๐ฎ ๐๐š ๐ง๐š๐ฆ๐ข๐ฃ๐ข ๐ญ๐š๐ค๐ž ๐ซ๐š๐ฌ๐š ๐›๐ฎ๐๐ฎ๐ซ๐œ๐ข๐ง๐ญ๐š ๐›๐š.
๐ค๐ฎ๐ฒ๐ข ๐ก๐š๐ค๐ฎ๐ซ๐ข ๐๐š ๐ฆ๐š๐ญ๐š๐ฒ๐ž๐ง๐ค๐ฎ ๐š ๐๐ฎ๐ค ๐ฒ๐š๐ง๐๐š ๐ฌ๐ฎ๐ค๐š ๐ณ๐จ ๐ฆ๐š๐ค๐ฎ.

๐€๐ฒ๐ข ๐ก๐š๐ญ๐ญ๐š๐ซ๐š, ๐€๐ฅ๐ฅ๐š๐ก ๐ฒ๐š ๐ซ๐ฎ๐Ÿ๐š ๐š๐ฌ๐ข๐ซ๐ข ๐ฒ๐š ๐ค๐ข๐ฒ๐š๐ฒ๐ž

๐š๐ฆ๐ž๐ž๐ง.

MINENE CIWON CIN RUWAโ“โ“Daga: Arrida Chemist๐Ÿ’ŠShinkafiDa farko ina yima kowa barka da JUMA'A๐Ÿ•Œ๐Ÿ•ŒDuba da yanayin damuna da mu...
27/08/2021

MINENE CIWON CIN RUWAโ“โ“

Daga: Arrida Chemist๐Ÿ’ŠShinkafi

Da farko ina yima kowa barka da JUMA'A๐Ÿ•Œ๐Ÿ•Œ

Duba da yanayin damuna da muke ciki naga ya dace in dan yi taqaitaccen bayani akan wannan cuta.

Amsa:- Shi cin ruwa cuta ce da wata kwayar cuta mai suna Fungus a turance ke haddasawa. Shi wannan Fungus din ana kiranshi ( tinea ) a turance. Kwayan cutar tana bukatar waje mai danshi da dumi-dumi don yaduwa k**ar yadda danshi ke samuwa tsakanin yatsun kafa.
Ita wannan kwayan cuta ta ( tinea ), itace ke kawo cutan makero na kai, ko wani lokacin ta kawo kaikayin matsematsi.

YADDA AKE KAMUWA DA CUTAR

shi ciwon cin ruwa da sauran nau'uka na irin wannan ciwo na fungus yana yaduwa daga mutum zuwa mutum, ko daga dabba zuwa mutum. Ko wajen amfani da safar kafa, ko tawul na wanka, da mai ciwon yayi amfani da shi. Kuma idan mutum na da ciwon a wani bangare na jikin shi, yana iya yaduwa zuwa wani bangaren. Kamar daga kafa zuwa matsematsi.

MAGANI:

Don maganin ciwon cin ruwa ana iya amfani da wani mai ko hoda da take da sinadarin maganin "anti fungus" ciki. Amma fa sai an shafa har kusan na wata daya zuwa sati shida kamin a warke.

KARIYA:

Ko da an warke ana iya sake kamuwa.

Wasu hanyoyin da ake bi wajen neman kariya sun hada da:
A tabbatar da tsakanin yatsu na cikin tsafta kuma a bushe ko yaushe.
Yawan canza safar kafa
Barin amfani da safa ko
Tawul da wadansu ke amfani da Ita.
Idan kana wajen tafki ( rafi, kududufi ko wajen wanka na gamagari ), A rinka sanya takalma.

Allah yakaramuna lafiya

LIKITA SHIN YAWAN SHAFA (FUNBACT A) A FUSKA A KO YAUSHE YANADA ILLA? DAGA: Arrida Chemist๐Ÿ’ŠShinkafiMaida magani abun amfa...
23/07/2021

LIKITA SHIN YAWAN SHAFA (FUNBACT A) A FUSKA A KO YAUSHE YANADA ILLA?

DAGA: Arrida Chemist๐Ÿ’ŠShinkafi

Maida magani abun amfani a koda yaushe ba don lalura ba hadarine tabbas yawan shafa magani bada wata laluraba ko kuraje Wanda ya danganci cream na kurajen fuska babban
hadarine Wanda ze kodema maki fuska
ya lalata ta, sanadiyar yana kashe wasu
kwayoyin sinadarin fata Wanda kusan
matanmu na hausawa sun maidashi yin
bleechin da kuma hasken fuska Wanda
hadarine da kashe sinadaran dake cikin
fuska masu taimak**a fata wajen
kofofin fitowar zafi da sauransu

Wanda kusan anyi funbact A da sinadarin
Funbact a Cream is used for

1.Itch or
2.rash
3., Bacterial infections ,
Ana amfanidashi wajen kashe ko Treatment of

1.(Ringworm ) k**ar kurajen hannu masu kada kuturta
2.(Skin inflammation), k**ar kashe cuta maisa fata kumburi
3.(Relief of itching), kashe kaikayi
4.(burning ), konewa
5.(Eczema) kyasfi
6.(Fungal skin) kurajen fata
(e.t.c

BABBAN AMFANIN FUNBACT A

1.kashe kurajen fuska
2.skin rashes
3.skin eczema
4.ubandawaki a fuska
5.bacteria soap
6.anti implamation
da sauransu

Illlar da yawan shafa funbact A yakeyi
badan wata cutaba

1.Idan kika samu rauni a fuska bazata
dunku ba wato idan akazo dinki fatar
bata dunkuwa
2.kashe sinadari me amfani a fatar jiki
3.irritation
4.swelling
5.redness
6.skin atrophy
7.burning
8.itching
9.allergic dermatitis
10.skin fever
da sauransu

DON ALLAH MATA A KIYAYE DA YAWAN
SHAFE SHAFEN. MAGANI BARKATAI BA
DON WATA CUTABA SEDAI DON WANI
AMFANI KAMAR
1.saka hasken fuska
2.gyaran jiki domin kara kyawo
babbar illa yake haifarwa

ALLAH YA KYAUTA

PRURITUS  (ALLAGIC REACTION ).A HAUSANCE MUNA IYA CEWA ๐Ÿ˜ SAMIHA๐Ÿ˜ SABODA WANNAN LOKACI NA DAMINA ZAMUYI BAYANI AKAN WANNAN ...
25/06/2021

PRURITUS (ALLAGIC REACTION ).
A HAUSANCE MUNA IYA CEWA ๐Ÿ˜ SAMIHA๐Ÿ˜ 

SABODA WANNAN LOKACI NA DAMINA ZAMUYI BAYANI AKAN WANNAN CUTA

Daga: Arrida Chemist๐Ÿ’ŠShinkafi

SAMIHA: wata wata cutace me adabar jama' a da dama, mussaman lokacin damina wani conditions ne da yake acikin jini Wanda hausawan Mu wani lokaci Sukeyi mata lakabi da iska Saboda idan tafitar da kuraje kuma bayan yan mintuna takoma

BABBAR MATSALAR DAKE FARUWA ITACE

mafiyawanci mutane idan basuda lafiya se su tsaya a gida aita magani ko su aika yaro chemist ya sawo masu priton
babban kalubale dake afkuwa shine

MATSALAR TSAYAWA GIDA KO AIKA YARO CHEMIST

1.farin farawa da ka tsaya gida kana yan shaye-shayen magani ko ka aika yaro chemist, bema san haqiqanin matsalarkaba se kawai ya afk**a magani kuma yin hakan illace

2.idan katsaya a gida za a sanya maka magani a Ruwa kayita kwankwada wani lokacima idan kanada hepatitis B ba'a la'akari da hakan.

3.Tsayawa gida sai aita magani daban ciwo daban

Samiha tana da illoli da yawa sosai saboda acikin jini take

MAFIYAWANCINTA BA A SAN ABUNDA.KE
HADDASATABA,
KAWAI DAI ANAYIN LA AKARI DA ANA GADONTA NE (INHERITED)

Allergic reaction rashes occur when
individuals come into contact with one
or more allergens that affect the skin.
These allergens do not necessarily have
to come into contact only with the skin.
Skin allergens can come from a variety of
sources and manifest in many ways.
Causes of Allergic Reaction Rashes
An allergic reaction can affect nearly
anyone at any time. Allergies may begin
at birth or at a time later in life. This
means that there are a number of
possible causes for an unexpected rash.
The following are just some of the most
common reasons for allergic reaction
rashes.

ALAMOMIN SAMIHA YANDA ZAKA GANE KANA DAUKE DA ITA

1.ciwon ciki me tsanani
2.diarrhea zawo
3.fitar kuraje da saurin bacewarsu
4.vomiting amai
5.kaikayi sosai
6.ciwon kai

TREATMENT A GIDA ILLANE
wani lokacima idan tafitoma mutum

1.sekaga yana wankada toka
2.shan ruwan toka
Wanda hakan yanada illa ga rayuwarmu

SHAWARWARI

IDAN BAKIDA KO BAKADA LAFIYA
GANIN LIKITA SHINE MAFITA
KADA KA TSAYA A GIDA AITA CIWO DABAN MAGANI DABAN.

ALLAH YASAUDACE

SHIN LIKITA KO MACCE ME CIKI (JUNA BIYU) TANA IYA YIN AL' ADA, KAMAR YANDA TA SABA NA WATA-WATA โ“Daga: Arrida Chemist๐Ÿ’ŠSh...
28/05/2021

SHIN LIKITA KO MACCE ME CIKI (JUNA BIYU) TANA IYA YIN AL' ADA, KAMAR YANDA TA SABA NA WATA-WATA โ“

Daga: Arrida Chemist๐Ÿ’ŠShinkafi

๐Ÿ•ŒBARKA DA JUMA'A๐Ÿ•Œ

A'a hakan baze yiyuba idan macce me
ciki tafara ganin jini to wannan alamun
matsalane wanda cikin ma yana iya zubewa wato (miscarriag)

A gaskiya idan Macce tana dauke da juna 2
tabbas bazata taba yin al' ada ba saboda al'ada tana zuwane kawai ga macce wadda
batada Ciki. duk bayan wata 1/ kokuma kwana 28

TABBAS IDAN MACCE ME CIKI TANA GANIN JINI LOKACIN DA TAKE DA CIKI
WATA 2/ KO 3 HAR ZUWA 4 TO GASKIYA AKWAI MATSALA

Saboda macce me CIKI batayin al' ada hasalima idan macce me ciki tafara ganin alamun zubar jini a jikin ta (al'aura) to tayi gaggawar daukan mataki saboda ba al' ada bace, alamun zuwan wata matsalace

TO LIKITA MIKESA ZUBAR JININ BA LOKACIN
AL' ADA BA

Matsalolin dake kawo jubar jini ga macce

1. miscarriage alamomin yin bari ko zubewar ciki

2.ectopic pregnancy( ciki bayan mahaifa )

3.placenter problems

4.infection of the placenter(kwayoyin cuta cikin mahaifa)

5.molar pregnancy (k**ar ciki. karya)

SHAWARA GA ME CIKI IDAN TANA GANIN JINI
YANA ZUBAR MATA

1. Gaggawar zuwa ganin likita domin baki kulawa wadda tadace
Saboda ayimaki photo agani idan cikin
rabinsa ya zube kokuma da
sauransa

2. A Gujema da tsayawa gida ayi treatment
Saboda tsaya gida babban hadarine Saboda idan juna biyu rabinsa ya zube aka bar sauranshi bai zubeba duka, sai kikasha maganin tsaida zubar jinin to ze iya
haifar maki da cuta kokuma.toshewar mahaifa kokuma molar gestation Wanda akecema kwanci

ABUBUWAN DAKE YAWAN SA BARI
(MISCARRIAGE)

1.yawan shan Abu me daci sosai

2.yawan saduwa lokacin da ciki yake dan
karami

3.yawan aikin wahala da dauka. Abu
me nauyi

4.yawan shan maganin Hausa barkatai

5.yawan shan magani na kwaya bada izinin
likitaba

6.infection (kwayoyin cuta su shiga mahaifa)
da sauransu

ALLAH YASA MUDACE

MENE NE CIWON SANฦ˜ARAU ?, YA AKE KAMUWA DA SHI ?, TAYA AKE KARE KAI DAGA KAMUWA DA SHI โ“Daga: Arrida Chemist๐Ÿ’ŠShinkafiMun...
21/05/2021

MENE NE CIWON SANฦ˜ARAU ?, YA AKE KAMUWA DA SHI ?, TAYA AKE KARE KAI DAGA KAMUWA DA SHI โ“

Daga: Arrida Chemist๐Ÿ’ŠShinkafi

Mundawo daga hutu
Muna yima kowa barka da ๐Ÿ•ŒJUMA'A๐Ÿ•Œ

A sak**akon shigowar zafi mu fara samun bullowar cutar sankarau a garuruwa da dama, wanda kuma sanin kowane cewa sankarau yakanyi muguwar barna cikin kankanin lokaci idan ba'a dauki matakin kariya ba.

FARKO: To wai shin ma menene Sankarau?

Sankarau wani nau'in ciwo ne da kwayoyin cuta ke mamaye mayafin da ke lullube kwakwalwa da lakar wuya da gadon baya. Wato (Meningitis) a turance.

Akwai nau'o'in ciwon sankarau daban-daban wanda kwayoyin cutar bacteria ne da ake kira Neisseria meningitis ke kawo nau'in sankarau din da muka fi sani

Su wadannan kwayoyin cuta suna nan a cikin iskan da muke shaka mai zafi

Hasalima kashi daya cikin biyar a cikin mu masu lafiya muna dauke da kwayoyin wannan ciwo a hancin mu da makogwaron mu bamu sani ba

Ta haka ake ya dasu idan anyi kaki an tofar ko kuma ta iska a wurin cin koso

Kwayoyin cutar mutuwa suke da sun ji sanyi. Don haka da wuya ayi sankarau lokacin sanyi

Idan aka shake su ta hanci kwayoyin na samun shiga jiki har jini ya kwashe su ya kai mayafin kwakwalwa

Nan da nan alamomin ciwon zasu bayyana

Su wa ciwon Sankarau yafi k**awa?
Bincike ya nuna cewa ciwon yafi k**a yara 'yan shekaru biyar zuwa goma 5-10, amma a lokacin annoba zai iya k**a kowa da kowa

ALAMOMIN CIWON SANKARAU!

1. Ciwon kai mai tsanani.
2. Zazzabi.
3. Sankarewar wuya.

Da zarar anji wadannan alamomi na farko sai ayi maza a nemi likita.

Idan an dade ba'a samu agajin likita ba, za'a ga mara lafiyar ya fara sankarewa........

MATAKAN KARIYA DAGA SANKARAU

1. A Daina bacci wurin da yake da zafi sosai
2. Idan akaje ganin mai dauke da cutar a sanya nose mask a rufe hanci da baki
3. Idan akayi ma'amula da kayan mai dauke da cutar to a wanke hannaye sosai.
4. Kuma a wannan lokaci na zafi a dinga wanka akai-akai

Allah ya karemu

AZUMI YANADA AMFANI SOSAI๐Ÿ’ฏ GA LAFIYAR DAN ADAMDaga: Arrida Chemist๐Ÿ’ŠShinkafi---------------------------------------------...
21/04/2021

AZUMI YANADA AMFANI SOSAI๐Ÿ’ฏ GA LAFIYAR DAN ADAM

Daga: Arrida Chemist๐Ÿ’ŠShinkafi
-------------------------------------------------

1. Azumi yakan hana mutum samun ciwon siga. Azumi yakan zama wani kafa na rage takuran sinadarin โ€˜Calorieโ€™ wanda kuma ze rage yiwuwan samu ciwon siga.

2. Azumi yakan taimaka wajen rage kiban jiki.
Azumi kan taimaka wajen rage kiba kuma ya kan kara konewan abinci da kashi 3.6% zuwa 14%.

3.Azumi yakan hana tsufa da wuri
Azumi kan rage tsufan jiki kuma yakan sa mutum ya dade a duniya cikin cikakken koshin lafiya.

4.Azumi na kara kaifin kwakwalwa
Azumi kan kara girman sinadarin jiki wanda ze taimaka wajen kara kaifin kwakwalwa.

5.Azumi kan kara girman naโ€™urar jiki wanda akafi sani da โ€˜Hormoneโ€™

Allah ya karbi Ibadunmu๐Ÿ™๐Ÿป๐Ÿ™๐Ÿป

๐Ÿ’”KORAFI DANGANE DA SAURIN INZALI๐Ÿ’”[PREMATURE EJACULATIONS]Daga : Arrida Chemist๐Ÿ’ŠShinkafiNa taba yin wannan bayanin a baya...
07/04/2021

๐Ÿ’”KORAFI DANGANE DA SAURIN INZALI๐Ÿ’”
[PREMATURE EJACULATIONS]

Daga : Arrida Chemist๐Ÿ’ŠShinkafi

Na taba yin wannan bayanin a baya
Amma tambayoyin mutane Akan hakan suna qaruwa ko yaushe. don haka kuji kuma ku
Karu.
Ace maigida baya jimawa sosai sai yayi release To lalle akwai matsala, da yawan maza suna fuskantar wannan matsalar (75%)
Illa Kawaidai s**an ji kunya ko nauyin yin
tambaya tare da zuwa neman magani wanda hakan Kuma bai k**ata ba, wasu ma suna ganin k**ar ba matsalar da za'a nemi
Likita bace inta k**a, kuma kuskure ne
hakan.

Abu na farko tsakani da Allah A ilmance ya k**ata kusani bafa duk kowane saurin release ke nuna maigida baida cikakkiyar lafiyar jima'i ba domin kwayoyin halittar mu sun bambanta da juna Kuma suna da tasiri aKan haka
matuqar dai mutum ba wata matsala
yasan yana da ita ba, ko wani Abu da
yasan yanayi k**ar ma********on da
sauransu.
Akwai wanda a halittar sa adrenal glands dinsu ke acting da sauri (wani sinadari ne) da zarar s**ai ido biyu da iyalansu a irin
wannan yanayi.

SHIN YA JIMA'IN MA YAKE ?

Yawan jima'i na cutar da jiki, don haka tazarar kwana 3 yaKan zama normal matukar Ana samun tazarar awa 72 kwana 3 shi kansa sinadarin s***m din shi zaisa ya zamto mai karfi da lafiyar da ciki zai iya shiga nan da nan bawai kullum kullum ba.

A bisa binkicen masana kusantar
Iyali yaKan fara zama kusanta ne daga
zarar ansami secons talatin da uku
(33secs).
Mafi karantar jima'i a ilmance
shine wanda yake farawa ya kare iya
minti daya zuwa biyu.
Matsakaici Kuma gamsashe bai
wuce minti bakwai da secons 4 hade da
wasanni da s**an tada sha'awa wanda bai
wuce na minti 2, saboda haka Inka cire
minti 2 cikin 7 saura biyar da secons
Arba'in (5.4minutes) wannan 5.4minute
shine normal duration da akan dauka
dan haka ba daidaine minti biyar ace
namijin baida lafiya ba illa dai ya dage
da service din kansa domin k**ar injin
ne dole Saida service.

Sai Mafi dogon zango shine daga
minti 10 zuwa 30, wanda wannan
shiyafi karanci saboda bakowa ne cikin
mutane keda kwayoyin halitta masu irin
wannan super power din ba hasali ma
bawai Basu release bane A'ah suna iya
Yi cikin minti 5 ma Amma suna da saurin
Kuma daukar caji kafin ma su ankara sai su koma.
wannan shine yasa.

SHAWARAR DA ZAN BAKU!!!

Abun Yi shine maigida idan kanayin
foreplay kadan to kara tsawon lokacin
wasanka da iyalinka hakan zaisa matarka ta daina jin cewa kana cutar ta.
Sannan itama macen idan har yana yawan
riganki release to ki taimaka ki nuna masa inda
in aka taba ajikinki kin fi saurin INZALI
hakan zai taimakeshi ya hada miki da
wannan sai kiji kuna samun gamsuwa
tare fiye da ki zuba mai ido saidai shi
yake taba ki walau kinajin dadin hakan
ko a'a.
Duk wani fruits ko vegetables da
kukasan yana da natural sugar Ku
Yawaita cinsa hakan nada mahimmanci
wato k**ar su (mangoro, lemon zaqi,
kankana, ayaba ds).
Haka dai idan ana fuskantar wannan
matsala ta saurin release to ka koma
kasa ya zamto Kaine akasa matar
asama hakan yaKansa asami Karin lokaci
kafin release.
Ka riqa yin stamina boost exercise.
Wato motsa jiki ta hanyar karfafa
tsokokin cinyarka da mara. Yadda ake
shine ka zauna saika hade kafafunka
guri daya ka dogare su saika sa
hannuwa ka rungumo kafafun kana
koma da baya kana kwanciya kana
dagowa kaita yin haka har sai kaji ka
fara gajiya.
Ka da ka riqa zuwa mata gado da
tunani ko damuwa akan wani Abu
(stress ko depression) ka tattare
dukkan wasu al'amuran rayuwa gefe
sannan ka tunkari wannan al'amrin
hakan zaisa ka sami stamina.
A riqa canza yanayin kwanciya kada ku
zamo kullum da anyi rigingine shikenan
sai kace kaji. A riqa caccanza pose hakan
na takaita ej*******on da sauri.
In kaji zaka kawo saika tsaya ka
jawo waje in kaji abun ya koma sannan
ka koma hakan yakansa adan sami Karin
time.๐Ÿ™ˆ๐Ÿ™ˆ๐Ÿ™ˆ

~~~~~Bincike ne

Allah ya kara Muna lfy.

๐ŸทMALTINA DA PEAK MILK BASU KARA JINI A JIKIN DAN ADAM:Daga: Arrida Chemist๐Ÿ’ŠShinkafiDa farko:- Inayi maku barka da JUMA'A...
26/03/2021

๐ŸทMALTINA DA PEAK MILK BASU KARA JINI A JIKIN DAN ADAM:

Daga: Arrida Chemist๐Ÿ’ŠShinkafi

Da farko:- Inayi maku barka da JUMA'A ๐Ÿ•Œ

Dayawa za kaga mutanen mu hausawa a lokacin da aka tabbatar da mutum yana da karancin jini, ko macce tana dauke da juna biyu, ko ta Haihu ta zubar da jini da yawa sai kaji ance a bata maltina da peak milk, a fahimtar mutanen mu zai kara jini.

Gaskiyar magana babu alaka tsakanin karin jini da Maltina da Peak milk, to ku sani waken muke ci kwara daya yafi Maltina da Peak milk wajen samar da sinadaran kara jini.

Nasan zakuyi mamakin maganata, to ba abun mamaki bane~~~Bincike ne~~Kayi tambaya idan baka gane ba.

Idan kun duba jikin gwangwanin peak milk za kuga babu sidaran karin jini a ciki ( not rich in iron) Haka Maltina ma Babu sinadaran kara jini a cikin ta.

Tambaya anan shine ta Ina Maltina da Peak milk s**a zama maganin karin jini ?

Amsa: wannan kawai al'adace ta mutanen mu ba tareda sanin abun ba.

Maltina na dauke da sinadaran:
- Calories
- Carbohydrates
- Fat
- Vitamin
- No Iron

Peak milk na dauke da sinadaran:
- Fat
- Carbohydrates
- Protein
- Salt
- Vitamin A and D
- No Iron

Jikin dan Adam yana samar da jini da kansa, shi jini yana bukatar sinadaran iron daga cikin abincin da muke ci yake samo shi.

Daga karshe ina bada shawara garemu kudin da muke kashewa wajen Maltina da Peak milk domin kara mana jini, muyi amfani da su wajen sayen abinci masu dauke da iron k**ar :

- Wake
- kifi
- Nama
- kwai
- Kaza
- Fara
- zogala (yar makka)
- cavage
- salat
- da sauran su.

Allah ya kara mana lafiya da zama lfy.

21/03/2021

Address

Bayan Gidan Gona Alkalawa
Shinkafi
3132

Telephone

+2348037465201

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Arrida Chemist Shinkafi posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Share on Facebook Share on Twitter Share on LinkedIn
Share on Pinterest Share on Reddit Share via Email
Share on WhatsApp Share on Instagram Share on Telegram