25/03/2026
Nasara daga Allah
ayau membobin Kungiyar Gyara kayanka youth foundation Dandin-mahe (Hisbah) sunyi Zama na musamman domin Kara inganta ayyukansu tareda fitowo da sabbin tsare-tsare
Acikin zaman Wannan Kungiya Mai albarka sunyi bita akan shawarwarinda s**a samu daga jami'an tsaro da shugabannin gari da malaman addini
Daga karshe Wannan Kungiya tayi addu'a zuwaga mutanen kirki wadanda sukewa wannan Kungiya fatan alkhairi
Bayan kammala wannan zaman membobin Wannan Kungiya sun zagaya wajen aiki (operation) domin tabbatarda tarbiyya da bin doka da oda da taimakawa wajen samarda tsaro domin taimakawa jami'an tsaro
Allah ya taimake gaskiya ya rusa karya da makaryata a Duk inda suke